Kotu ta aike wa shugaban gidan yari sammaci a kan hana El-Zakzaky ganin likita

Kotu ta aike wa shugaban gidan yari sammaci a kan hana El-Zakzaky ganin likita

Babban kotun jihar Kaduna, a jiya ta aike wa shugaban gidan gyaran hali na jihar sammaci saboda hana shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), Ibrahim El- Zakzaky da matarsa, Zeenat ganin likitocin da suka zaba.

Alkalin, Mai shari'a Gideon Kurada a zaman kotun karo na shida a ranar 6 ga watan Fabrairun 2020 ya bayar da umurnin a kyalle wadanda ke kare kansu daman ganin likitansu da suka zaba a gidan gyaran halin na Kaduna karkashin kulawar jami'an gidan gyarar halin.

Amma a zaman kotun na jiya, kotun ta jinkirta sauraron shari'a zuwa 12 na rana domin jin ta bakin shugaban gidan yari a kan dalilin da yasa aka hana El-Zakzaky ganin likitansa a lokacin da ake tsare da shi. Daya daga cikin lauyoyin El-Zakzaky, Abubakar Marshal da farko ya fada wa kotu cewa an hana Zeenat ganin likitanta kamar yadda kotun ta ba ta dama.

Kotu ta aike wa shugaban gidan gyaran hali sammaci kan hali El-Zakzaky ganin likita
Kotu ta aike wa shugaban gidan gyaran hali sammaci kan hali El-Zakzaky ganin likita
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Mu na alfahari da almajiranci, bai kamata a hana ba - Adamu Garba

A lokacin da aka tashi zaman kotun a jiyan, lauyan ya shaidawa manema labarai cewa shugaban gidan yarin ya bayyana gaban kotun inda ya shaida wa kotun dalilan da yasa ya hana likitan ganin su El-Zakzaky da matarsa.

A bangarensa, lauyan gwamnatin jihar Kaduna wanda shi ne jagoran lauyoyin da suka shigar da karar El-Zakzaky, Dari Bayero ya ce kotun ta bawa wadanda suke kare kansu daman ganin likitocinsu saboda ba za a samu wata matsala ba a lokacin da za a gudanar da shari'arsu a ranakun 23 da 24 na watan Afrilu.

Ana tuhumar El-Zakzaky da matarsa da aikata laifuka takwas da suka hada da zargin kisa, yin haramtaciyyar taro, tayar da zaune tsaye, hadin baki domin aikata laifi da wasu laifukan da gwamnatin jihar ta Kaduna ke tuhumarsu da aikatawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel