Jam’iyyar APC ta shawarci PDP ta koma noman shinkafa tunda ba ta da aikin yi

Jam’iyyar APC ta shawarci PDP ta koma noman shinkafa tunda ba ta da aikin yi

Jam’iyyar APC mai mulki ta shawarci yayan jam’iyyar PDP su koma gona su rungumi noma shinkafa tunda dai basu da aikin yi, kamar yadda mai magana da yawun jam’iyyar, Malam Lanre Issa-Onilu ya bayyana.

APC ta bayyana haka ne a matsayin raddi ga bukatar jam’iyyar PDP ga kotun koli inda ta nemi kotun ta sake duba shari’ar zaben shugaban kasa tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da dan takararta Atiku Abubakar domin ta sake gudanar nazari game da hukuncin.

KU KARANTA: Azumin jama’an Borno ya fara aiki: Mayakan ISWAP sun kashe kwamandojinsu guda 3

Baya ga wannan, haka zalika PDP ta bakin mai magana da yawunta, Kola Ologbondiyan ta nemo kotun koli ta sake duba hukunce hukuncen da ta yanke a shari’un zabukan gwamnonin jahohin Osun, Kano, Kaduna da Katsina, kuma ta sake nazarin hukunce hukuncen.

Sai dai Kaakakin APC ya bayyana PDP a matsayin jam’iyyar da ta shiga rudani tun bayan da yan Najeriya suka yi fatali da ita a zaben 2015, wanda hakan yasa ta zama abin dariya a siyasar Najeriya.

“Ba’a taba samu a tarihin siyasar Najeriya wata jam’iyya da ta mayar da hamayya abin dariya kamar yadda PDP take yi ba, wannan bukata na PDP ya tabbatar da matsayarmu a kanta na cewa it ace ta lalata siyasar kasar nan, ta hanata cigaba.

“Muna da yakinin wasu shuwagabannin PDP sun gagara samun sukuni tun bayan sauka daga madafan iko, da alama akwai yan banza da yawa a sakatariyar PDP Wadata House, shawararmu ita ce a wannan lokaci da gwamnatinu ke kokarin samar da isashshen abinci a Najeriya, muna kira ga yan zaman banza a PDP su koma noman shinkafa sai sun fi ma kasa amfani a haka.” Inji shi.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki ta yini guda jahar Ondo domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin jahar ta kammala a karkashin jagorancin Gwamna Rotimi Akeredolu SAN.

Gwamna Rotimi da kansa tare da manyan jami’an gwamnatinsa ne za su tarbi shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da yan tawagarsa, inda shugaban zai kaddamar da wani katafaren gadar sama da cibiyar masana’antu a garin Ore, na karamar hukumar Odigbo.

Ana sa ran jagoran jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jahar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu na daga cikin wadanda zasu raka shugaba Buhari zuwa Ondo, kafatanin gwamnonin jahohin yarbawa 6, ministoci daga yankun Yarbawa da kuma yan majalisu daga jahar Ondo duk zasu halarci taron.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel