Zargin Almundahanan: N1.35bn Shaidu sun kara bayyana gaban kotu kan Sule Lamido

Zargin Almundahanan: N1.35bn Shaidu sun kara bayyana gaban kotu kan Sule Lamido

- Ana cigaba da shariar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido

- Ana zarginsa da almundahanar makudan kudin alummar jihar Jigawa lokacin ya mulki jihar

- Ya yi mulkin jihar ne tsakanin 2007 da 2015

Daya daga cikin jami’an hukumar hana almundahan da yiwa tattalin arzikin kasa da hana zagon kasa(EFCC), Michael Wetkas, a ranar Alhamis, 20 ga watan Febrilu 2020, ya yiwa kotu bayanai akan yadda tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido ya karkatar da wasu kudade na aikin Jihar zuwa kamfanin Dantata da Sawoe dan bukatar kansa.

Kakakin hukumar EFCC, Tony Orilade, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Lahadi.

A cigaban shari’ar yau, Wektas ya bayyanawa kotu cewa bincikensu ya nuna yadda kamfanonin Lamido suka samu daruruwan miliyoyi dake shiga asusun bankinsu ta hanyar cak da Kamfanin Dantata da sawoe suka bayar a tsakanin 2007 da 2013.

Wektas ya bayyana cewa an fitar da kudi N7,408,000 da N7,425,000 daga asusun kamfanin Dantata da Sawoe na bankin Zenith a ranar 5 ga watan Maris 2013 zuwa asusun kamfanin Barmania.

Har ila yau, Mai bada shaidar ya bayyana cewa a ranar 23 ga watan Afrilu 2013, akwai cak guda biyu na N7,228,900 daga asusun bankin Zenith da aka bayar da zuwa asusun Speeds international limited.

Wektas ya cigaba da bayyanawa kotu cewa an baiwa Speeds International limited kimanin N9,450,000 a ranar 19 ga watan oktoba, 2019 da kuma da wasu daga asusun Kamfanin Dantata da Sawoe na bankin UBA da Access zuwa kamfanonin Alhaji Lamido.

Alkali Ojukwu ya dakatar da al’amarin zuwa karshen da farkon watan mayu domin cigaban shari’ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel