Yaki da rashawa: Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 160 ga wata Mata da abokanta 3

Yaki da rashawa: Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 160 ga wata Mata da abokanta 3

Wata mata mai suna Hadiza Bello tare da abokanta guda uku sun gamu da hukuncin daurin shekaru 160 a gidan gyaran halayya biyo bayan kamasu da aka da laifin damfara da kudin bogi, inji rahoton Punch.

Majiyarmu ta ruwaito babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Yola na jahar Adamawa ne ta yanke musu wannan hukunci bayan hukumar yaki da rashawa da makamanta laifuka, ICPC, ta gurfanar dasu a gabanta.

KU KARANTA: Fayose ya yi fatali da batun komawarsa cikin jam’iyyar APC

Wata sanarwa daga bakin kaakakin ICPC, Rasheedat Okoduwa ta bayyana cewa Hadiza Bello, Mohammed Daudu, Bello Salisu, Ali Adamu da Hassan Bello sun shirya damfarar wani jami’in kwastam ne, inda zasu bashi naira miliyan 5 na bogi, su kuma su amshi naira miliyan 1 mai kyau.

“Kotun tarayya dake zamanta a Yola ta yanke ma mutane hudu daga cikinsu har da wata mace hukuncin daurin shekaru 160 a kan tuhume tuhumen laifuka da danganci mallakar kudaden bogi.

“Mai Sharia Abdulazeez Anka ne ya yanke wannan hukuncin, inda ya zartar musu da hukuncin shekaru 10 a gidan yari bisa kowanne tuhuma daga cikin tuhume tuhume guda hudu da ICPC take musu, sai dai banda Hassan a cikin hukuncin sakamakon ya mutu kafin a kammala shari’ar.

“Mutanen hudu sun gana da Hassan Bello mai sana’ar bokanci a watan Maris na shekarar 2017 a gidansa dake Wamdeo jahar Borno domin ya basu kudin bogi na naira miliyan 5, su kuma su damfari wani jami’in kwastam dasu a kan kudi naira miliyan 1.

“Sai dai cinikinsu da kwastam din bai kullu ba, don haka suka juya zuwa Borno, amma a kan hanyarsu ta komawa a daidai Girei-Yola Sojoji suka kamasu dauke da kudaden bogi yan N1000 da suka kai N5,504,000, kuma suka mikasu ga ICPC” inji ta.

ICPC ta cigaba da gudanar da bincike har gidan bokan, inda ta gano karin kudaden bogi, daga nan ta gurfanar dasu gaban kuliya sakamakon laifin da take tuhumarsu ya saba ma sashi na 5(1)(b), 6(2)(b) kuma hukuncinsu na cikin sashi na 5(1)(c).

Da wannan ne Alkalin kotun ya yanke musu hukuncin zaman gidan kaso shekaru arba’in kowannensu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel