Boko Haram: An gudanar da Sallar nafila cikin azumi da adduoi a jihar Borno (Bidiyo)

Boko Haram: An gudanar da Sallar nafila cikin azumi da adduoi a jihar Borno (Bidiyo)

Ranar Litinin mutanen jihar Borno sun tashi da azumi da addu’o’i don neman mafita daga Allah kan hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram da suka addabi mutan jihar.

Hakazalika, an gudanar da Sallar nafila a babbar Masallacin Maiduguri.

Fiye da shekaru goma yanzu, ‘yan taaddan Boko Haram sun kai hallaka daruruwan mazauna jihohin Borno, Adamawa da Yobe kuma sun kori dubunnai daga muhallansu.

A makon da ya gabata ne Gwamnan jihar Borno Umara Zulum, ya bukaci al’ummar jihar da su yi azumi ranar Litinin.

Gwamna Zulum, ya kara da cewa Shehun Borno ya tabbatar masa da cewa duka limamai na kananan hukumomi 27 da ke jihar za su yi addu’o’i da Qunuti a duka salloli biyar na ranar Litinin.

Mun kawo muku rahoton cewa Yan ta'addan Boko Haram sun kona barikin yan sanda, cocina, gidan Janar Paul Tarfa da gidajen mutane a mumunan harin da suka kai jihar Adamawa ranar Juma'a, 21 ga watan Febrairu, 2020.

Majiya daga garin Gargisa, ya bayyana yadda yan ta'addan suka sace dukayar al'umma kafin bankawa gidajen wuta.

Yace: "Sun shigo da yawa, tare da motoci 14 suka dira garin; kuma suka sace shagunan sayar da magani da kayan abinci."

"Sun samu damar cin karansu ba babbaka saboda an janye bataliyan Sojin da ke garin kwanakin baya kuma aka bar wasu yan tsirarun Soji da suka gaza kawar da yan ta'addan."

"Bayan sace-sacen da sukayi, sun kona barikin yan sandan, cocina biyu na Living Faith da EYN, da kuma kantin kaya."

"Hakazalika an kashe mutane amma ban san adadinsu ba a yanzu."

"Kana sun kona gidan Janar Paul Tarfa, tare da gidaje masu muhimmanci a garin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel