Wata mata ta haifi 'yan tagwaye a layin karbar tallafi a Jigawa
- Wata mata ta haifa tagwaye a yayin da take kan bin layin karbar tallafin N-Power a jihar Jigawa
- Wata majiya ta sanar da cewa matar ta haifi yaro daya ne a lokacin da ake tantanceta inda ta kara sunkoto daya bayan an kaita wani gidan biredi da ke makwabtaka da wajen
- A jawabin shugaban shirin bada tallafin na N-Power, Malam Bala Chamo ya ce mutane 14,000 ne suka amfana da tallafin naira dubu biyar-biyar din
Wata baiwar Allah ta haifa tagwaye a lokacin da take kan bin layin karbar tallafin N-Power a kofar fadar hakimin Aujara, Malam Aminu Danmalam.
Matar mai suna Khadija Abubakar na da shekaru 35 kuma tana sana’ar kuli-kuli ne. Ta je karbar tallafin ne daga kauyen Gorarun inda ta haifi tagwayen yara maza a wajen.
Hakimin garin Aujara, Malam Aminu Danmalam, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.
Wata majiya ta sanar da cewa matar ta haifi yaro daya ne a lokacin da ake tantanceta. Ganin hakan ne yasa aka hanzarta kai ta wani gidan burodi da ke da makwabtaka da wajen inda ta sake haifo wani dan.
DUBA WANNAN: A garin neman gira: Matashi ya dirki kwayoyin karin kuzari, ya mutu yana lalata da budurwa
A jawabin shugaban shirin bada tallafin na N-Power, Malam Bala Chamo ya ce mutane 14,000 ne suka amfana da tallafin naira dubu biyar-biyar yayin da kuma mutane dubu dari ne za zu amfana da tallafin a jihar Jigawa.
Ya ce, kafin wannan lokacin, a baya ana ba mata 65,229 tallafin amma sai aka kara mata 34,771.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng