Abun kunya: An samu wani malami a Kano da ke nuna wa dalibansa mata fim din batsa a aji

Abun kunya: An samu wani malami a Kano da ke nuna wa dalibansa mata fim din batsa a aji

Babbar kotun jihar Kano mai lamba takwas ta saka ranar 19 ga watan Maris don sauraron shaidun shari’a kan wani malami da dalibansa. Mai shari’a Usman Na’Abba ya fara sauraron karar da ake tuhumar wani malami mai suna Adekunle Ilesonmi da laifin lalalta da dailbansa.

Adekunle dai mazaunin Kings garden ne kuma yana koyarwa ne a wata makarantar kudi da ke Sabon Gari a jihar Kano.

Anan zarginsa ne da lalata da dalibansa masu karancin shekaru har su uku. Kamar yadda tuhumar ta bayyana, Adekunle na yaudarar daliban nasa ne ta hanyar saka musu fina-finan batsa. Daga nan kuwa sai ya fara lalata dasu. Lamarin da malamin makarantar ya musanta aikatawa.

Kamar yadda gidan rediyon freedom da ke Kano ya bayyana, laifin nan ya saba da sashi na 283 na kundin penal code kuma hakan abun hukuntawa ne.

A halin yaznu dai mai shari’a Usman Na’Abba ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Maris na 2020.

DUBA WANNAN: A garin neman gira: Matashi ya dirki kwayoyin karin kuzari, ya mutu yana lalata da budurwa

Kamar dai yadda aka sani, malamai dai ana kai musu dalibai ne ba don koyon ilimi kadai ba, har da tarbiyya.

Abun mamakin da ban haushi shine yadda wasu bata-gari daga cikin malaman makarantar suke karewa wajen lalata tarbiyar da yaran suka zo da ita daga gida. A irin wannan halin kuwa, malaman kan manta cewa amana ce aka basu ta daliban wacce a bar tambaya ce a ranar gobe kiyama.

A wajen lalata tarbiyar da daliban suka zo da ita, ana bigewa ne da yin biyu babu. Babu karatun sannan babu tarbiyar. Sanannen abu ne idan aka ce ilimi ba ya zama inda babu tarbiya. Muna fatan masu ire-iren wannan halayyar su tuba kuma su daina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel