Ni gwamnan 'mu'ujiza' ne - Sanata Diri
Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya kwatanta kansa da gwamna mai cike da mu'ujiza. Gwamnan da ya zanta da manema labarai a Abuja a jiya Lahadi, ya tuna kalubalen da ya fuskanta kafin ya samu hakkinsa.
An rantsar da gwamnan ne a ranar 14 ga watan Fabrairun 2020, bayan kotun koli ta soke nasarar dan takarar jam'iyyar APC, David Lyon.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Diri ya ce: "mun sha ruwa kuma mun sha rana, amma a karshe Ubangiji da kansa ya kawo tallafi. Don haka zan kira kaina da Gwamna mai 'mu'ujiza'."
DUBA WANNAN: Nan da makonni kadan Boko Haram zasu zama tarihi - Buhari
"Maganar gaskiya shine, an hada sakamakon zabe ne a wani dakin otal da ke Yenagoa ta hanyar amfani da karfin tarayya don a kwace jihar Bayelsa. Amma kowa ya san na yi watsi da wannan sakamakon. Amma a yunkurin su na nuna cewa halastaccen sakamako ne, sai suka fara kitsa wa 'yan Najeriya labarai a kaina, wanda na gada da dai sauran labarai marasa tushe.
"Sun yi amfani da karfin tarayya ne wajen tura wa 'yan Bayelsa wanda suke so. Amma kuma abin farin cikin a yau shine, PDP tayi nasara kuma Bayelsa ta same ni. Wannan kuwa ya ci karo da burikansu." Ya ce.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng