Zargin kisan kai: Gwamnan Ebonyi ya mika hadimansa biyu ga hukumar Yansanda

Zargin kisan kai: Gwamnan Ebonyi ya mika hadimansa biyu ga hukumar Yansanda

Gwamnan jahar Ebonyi, David Umahi ya sallami wasu hadimansa guda biyu biyo bayan zarginsu da ake yi da aikata laifin kisan kai a yayin zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP na zaben shuwagabannin kananan hukumomin jahar.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito bugu da kari Gwamna Umahi ya mika mutanen biyu ga hannun hukumar Yansandan Najeriya reshen jahar Ebonyi domin su gudanar da cikakken bincike a kansu.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Kaduna ta kalubalanci hukuncin kotu na sakin yan shia 92

Umahi ya nemi Yansanda su gurfanar da mutanen biyu gaban kotu idan har sun samesu da hannu cikin kisan kai da ake zarginsu da aikatawa a yayin zaben fidda gwani na PDP a ranar Juma’a 21 ga watan Feburairu.

Sakataren gwamnatin jahar Ebonyi, Dakta Kenneth Ugbala ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 23 ga watan Feburairu a garin Abakaliki, inda ya bayyana sunayen hadiman gwamnan biyu da mukamansu.

Hadiman sun hada da mai kula da karamar hukumar cigaba ta Ubeyi Development Center cikin karamar hukumar Afikpo ta Arewa Misa Uche Ibiam da Iblam Ogbonnaya, mai taimaka ma gwamna a kan harkar tsaro.

Daga karshe gwamnan ya baiwa al’ummar jahar Ebonyi tabbacin tsaron rayukansu da dukiyoyinsu, tare jaddada manufarsa na cigaba da tabbatar da zaman lafiya da lumana a jahar.

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jahar Ekiti, Ayodele Fayose ya musanta jita jitan da ake yayatawa a kan wai zai fice daga jam’iyyar adawa ta PDP ya wankan tsarki zuwa jam’iyya mai mulki, jam’iyyar APC.

Jaridar BluePrint ta ruwaito mai magana da yawunsa, Lere Olayinka ne ya bayyana haka a madadin Fayose, inda yace mai zai yi da APC, jam’iyyar da ta kamu da cutar Coronavirus? Don haka yace APC ba irin jam’iyyar da mutum kamarsa zai iya shiga bane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel