Rijiyar burtsatsai 97 ga kowace karamar hukuma - Manyan ayyuka 6 da za’a iya aiwatarwa da kudi $100m da Bagudu ke son karba

Rijiyar burtsatsai 97 ga kowace karamar hukuma - Manyan ayyuka 6 da za’a iya aiwatarwa da kudi $100m da Bagudu ke son karba

A ranar Juma’a, Amurka ta nuna rashin amincewarta da shirin baiwa gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, kudi $110m na kudin satan da Abacha ya boye a kasar waje.

A baya, Abubakar Bagudu ya kasance mai bada shawara kan hannun jari ga tsohon shugaba Sani Abacha, kuma an zargin cewa shi ya taimakawa Abacha wajen sace kudin.

Takardun kotu sun bayyana cewa an yi wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da Bagudu a shekarar 2018 kan amsan nashi kason idan Amurka ta dawo da kudin.

KU KARANTA Ranar Laraba kotun koli zata yi zaman sake duba shariar jihar Bayelsa

TheCable ya lissafo manyan ayyuka shida da za’a iya aiwatarwa na jin dadin al’umma da kudin da Bagudu ke kokarin amsa.

1. Ajujuwan makaranta 13,480

A bisa lissafin kasafin kudi, za’a gina ajujuwa hudu a farashin N10m. Hakan na nufin cewa maimakon baiwa Bagudu kudin, za’a iya azuzuwa 13,480 a fadin tarayya.

2. Na’urar gwada cutar daji 37 da na’urar daukar hoto a asibiti 674

A farashin $3m ga kowani guda, za’a iya siyan na’urar gano cutar daji 37

Hakazalika za’a iya sayan na’urar daukar hoto a asibiti (Xray) 674 a farshin N60m ga kowani guda.

3. Rijiyar burtsatsai 97 a kowace karamar hukumar cikin kananan hukumomi 774 na kasa.

Ana hakan rijiyar burtsatsai a farashin N450,000, da kudi N33.7 billion, za’a gina rijiyar burtsatsai 74,889 kuma kowace karamar hukuma zata samu 97.

4. Da kudi N33.7bn, za’a iya sayan jiragen yaki JF17 Thunder mai farashin N4.3bn guda takwas domin yakan Boko Haram da yan bindiga.

5. Da kudin nan, maimakon matasa 500,000, za’a iya daukan matasan N-Power milyan daya kuma a rika biyansu 30,000 ba tare da matsala ba.

6. A cikin kasafin kudin 2020, za’a iya amfani da kudin wajen daukan nauyin ayyukan hukuma EFCC gaba daya na shekarar 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel