Kwankwaso ya jahilci yadda kotu ke aikin ta - Kwamishinan Ganduje

Kwankwaso ya jahilci yadda kotu ke aikin ta - Kwamishinan Ganduje

Gwamantin jihar Kano ta ce Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar 'ya jahilci yadda ake gudanar da shari'a' saboda neman cewa kotun koli ta sake bibiyar hukuncin da ta zartar na tabbatar da nasarar Abdullahi Ganduje a matsayin gwamnan jihar.

Kotun kolin a hukuncin da ta yanke a ranar 20 ga watan Janairu ta yi watsi da daukaka karar da Abba Kabir Yusuf, dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP ya shigar inda ya yi ikirarin cewa an tafka magudi a zaben.

Kwankwaso a ranar Laraba ya jagoranci wasu mambobin PDP daga jihar Kano zuwa sakatariyar jam'iyyar PDP na kasa inda ya nemi su mara masa baya wurin kira ga kotun koli ta sake duba zaben gwamna na jihar Kano.

Kwankwaso ya jahilci yadda kotu ke aikin ta - Kwamishinan Ganduje
Kwankwaso ya jahilci yadda kotu ke aikin ta - Kwamishinan Ganduje
Asali: Twitter

Da ya ke martani a kan batun, Kwamishinan Sadarwa na jihar Kano, Muhammad Garba cikin wata sanarwa ya ce: "Kiran da Kwankwaso ke yi ya nuna karara cewa ya jahilci yadda aka gudanar da shari'ar da ta tabbatar da nasarar Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin zababben gwamna."

DUBA WANNAN: Mu na alfahari da almajiranci, bai kamata a hana ba - Adamu Garba

Garba ya ce tsohon gwamnan na Kano ba shi da wata dalili na cewa a sake duba zaben na Kano saboda jam'iyyar PDP ta sha mummunan kaye ne a kotun koli.

Ya ce: "Hukuncin da kotun koli ta yanke ya yi dai-dai da hukuncin da kotun zabe da na daukaka kara suka yanke. Hakan na nuna cewa jam'iyyar PDP ta sha mummunan kaye kuma sun gaza gamsar da kotu cewa an tafka magudi. Saboda haka babu wata dalili na neman a sake duba zaben."

Kwamishinan ya ce kararrakin da aka shigar a kotun koli na neman sake duba zabukan gwamnan Imo da Bayelsa ne ya saka Kwankwaso ya bijiro da wannan bukatar sai dai akwai banbanci tsakanin abin da ya faru a Kano da sauran jihohin.

Ya kara da cewa kotun ba za ta canja hukuncin da ta zartar a kan zaben na Kano ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel