Satar waya: Kotun Najeriya ta yanke wa matashi Abdulkareem hukuncin kisa ta hanyar rataya

Satar waya: Kotun Najeriya ta yanke wa matashi Abdulkareem hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Wata babbar kotun jihar Ekiti ta yankewa wani mutum mai matsakaicin shekaru hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Mai gabatar da karar ya bayyana cewa wanda ake zargin ya dau adda da bindiga ne inda yayi wa wasu fashin wayar hannu da kudi

- Kamar yadda alkalin ya bayyana, ya ce masu gabatar da karar sun bayyana shaidun bindiga, harsasai da wayoyin da suka damke wanda aka yankewa hukuncin da shi

Wata babbar kotun jihar Ekiti ta yankewa wani mutum mai matsakaicin shekaru hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mai shari'a Mosunmola Abodunde a yayin yankewa Albdulkareem Isa hukunci a ranar Juma'a, ya ce masu gabatar da karar sun tabbatarwa da kotun laifin da wanda ake zargin ya aikata, a don haka kotun ta kama wanda ke kare kansa da laifin.

A yayin shari'ar, mai gabatar da kara daga ma'aikatar Shari'a, Gbemiga Adaramola, ya sanar da kotun cewa Abdulkareem ya dau bindiga da adda kuma ya yi wa Taiwo Olomola fashin N10,000 da waya kirar Tecno.

Satar waya: Kotun Najeriya ta yanke wa matashi Abdulkareem hukuncin kisa ta hanyar rataya
Satar waya: Kotun Najeriya ta yanke wa matashi Abdulkareem hukuncin kisa ta hanyar rataya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hana bara a Kano: Sheikh Isa Pantami ya bayyana matsayinsa

Adaramola ya ce Abdulkareem ya yi fashin ne a ranar 19 ga watan Disamban 2016 a yankin Ureje da ke Ado-Ekiti.

Ya ce, "Abdulkareem ya yi wa wani mai suna Adeya Olalekan fashin N74,000 da kuma waya kirar Infinix Note 2. Wadannan laifukan na fashi da makami sun ci karo da sashi na 402, sakin layi na 2 na dokokin Criminal Code na jihar Ekiti."

Abdulkareem ya musanta wadannan laifukan da ake zarginsa da su.

Wanda aka yankewa hukuncin an damke shi ne a yayin da yake aikata laifin tare da makaman wanda hakan ya kawo sauki ga 'yan sandan wajen kawo shaidu.

Mai gabatar da karar ya kawo shaidu hudu sannan ya kawo makaman da suka hada da bindiga biyu, harsasai masu rai biyu, wayoyi da kuma takardar da ta kunshi abinda wanda ake zargin ya sanar.

Adeyinka Opaleke ne ya wakilci wanda aka yankewa hukuncin kuma shi kadai ya bayyana a shaidar wanda aka yankewa hukuncin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel