Atiku ya yi magana a kan harin da Boko Haram ta kai Adamawa

Atiku ya yi magana a kan harin da Boko Haram ta kai Adamawa

Harin da 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram suka kai a wani sashi na jihar Adamawa a baya-bayan nan ya janyo hankalin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abukakar.

Atiku ya yi magana a ranar Asabar, 22 ga watan Fabrairu, inda ya ce hare-haren sun zama abin tsoro.

Atiku ya ce, "Hare-haren da Boko Haram ke kai wa ga rayuka da dukiyoyin'yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba ya kai wani mataki mai ban tsoro.

"Ina yi wa mutanen jiha ta na garin Garkidi addu'a a kan harin da ya faru a cikin karshen mako. Ina fata Allah ya bawa iyalansu hakurin jure rashin."

DUBA WANNAN: Kiris ya rage mu gama da Boko Haram da ISWAP: Buratai ya fadawa sojoji

Legit.ng ta ambaci wani rahoto da ya ruwaito cewa wasu 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kashe mutane da dama a Garkida, wani gari da ke karamar hukumar Gombi na jihar Adamawa.

An ruwaito cewa 'yan ta'addan sun kutsa cikin garin misalin karfe 7 na ranar Juma'a, 21 ga watan Fabrairun 2020 suna ta harbe-harbe.

A cewar rahoton, dakarun sojojin Najeriya da suka yi musayar wuta da 'yan ta'addan sun janye daga baya domin kara yin shiri.

Daga baya sojojin sun janye domin su sake shiri amma rahoton ya ce 'yan ta'addan shiga cikin garin inda suka kone gidaje masu yawa.

A bangarensa, gwamnan jihar Babagana Zulum ya bayyana wasu hanyoyi da za a bi domin yin nasara a yakin da gwamnatin tarayya ke yi da 'yan ta'addan.

A cewar rahoton, Zulum ya ce ana bukatar daukan sabbin sojoji kimanin 100,000 tare da siya wa sojojin makamai da wasu kayan aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel