Kotun koli ta tafka kuskure a yanke hukuncin kwace kujerar gwamnan Bayelsa - Falana

Kotun koli ta tafka kuskure a yanke hukuncin kwace kujerar gwamnan Bayelsa - Falana

Babban lauya a Najeriya, Femi Falana, ya yi martani a kan hukuncin da kotun koli ta yanke a kan zaben kujerar gwamnan jihar Bayelsa.

Yayin tattuanwarsa da gidan talabijin na 'Channels', Falana ya bayyana cewa babbar kotun ta yi kuskuren yanke hukunci bayan zabe a kan karar da aka shigar kafin zabe.

"Sashe na 133 na dokokin zabe ya bayyana cewa matukar aka kammala zabe har aka bayyana wanda ya samu nasara, duk wani korafi a kan yadda aka gudanar da zabe, ko a kan cancantar dan takara; alhakin kotun sauraron korafin zabe ne, watau 'Tribunal', ta saurara tare da daukan mataki, kotun koli bata da hurumi," a cewar Falana.

A ranar 13 ga watan Fabrairu ne kotun koli a karkashin jagorancin Jastis Mary Peter-Odili ta yanke hukuncin kwace kujerar gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon, na jam'iyyar APC tare da umartar hukumar zabe ta karbe shadarsa ta cin zabe ta bawa dan takarar jam'iyyar PDP.

Kotun koli ta tafka kuskure a yanke hukuncin kwace kujerar gwamnan Bayelsa - Falana
Femi Falana (SAN)
Asali: Depositphotos

Kotun ta soke zaben Lyon ne bayan samun abokin takararsa, watau dan takarar mataimakin gwamna, da laifin gabatar da takardu na bogi a cikin fom dinsa na takara da jam'iyyar APC ta mika wa hukumar INEC.

Hakan ne yasa kotun ta soke zaben tare da karbe nasarar da jam'iyyar APC ta samu da yin umarnin a mika kujerar gwamnan ga Sanata Douye Diri, dan takarar jam'iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Dan ta'adda ya kai hari Masallaci a London, ya yanka wuyan Ladani (Hoto)

Da yake martani a kan hukuncin da kotun ta yanke, Falana; mai yawan sukar manufofin gwamnatin tarayya ta APC, ya kafe a kan cewa kotun kolin ta tafka kuskure.

Ya bayyana cewa kotun koli bata da hurumin sauraron karar domin magana ce da ya kamata a shigar da ita a kotun sauraron korafin zabe.

A yayin da kotun kolin ke shirin sake duba hukuncin da ta yanke a kan karar, babba lauya, Falana, ya bayyana kwarin gwuiwarsa a kan cewa kotun za ta yi amfani da damar wajen kara karfafa dokokin kasa, kuma za ta yi abinda ya dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel