Fusatattun matasa sun kone motar 'yan sanda kurmus a Jigawa

Fusatattun matasa sun kone motar 'yan sanda kurmus a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da cewa an kone motar sintirinta wacce ta kashe wata mai tsallaka titi mai suna Hauwa Danladi-Turis. Motar ta raunata mutane hudu a karamar hukumar Malammadori ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, Abdu Jinjiri, ya sanar da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Malammadori, cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a.

Jinjiri, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da mota dauke da ‘yan sanda biyu take bin wata mota da take zargi.

“Dan sandan na bin wata mota ne da ake zargi kuma yayi kokarin kama ta ta gefe. A hatsarin da ya auku, motar ta make wata yarinya kuma ta mutu yayin da wasu mutane hudu suka raunata.

“A cikin rashin sa’a ne wasu matasa a yankin suka yi amfani da damar wajen bankawa ababen hawan biyu wuta a take,” ya ce.

Jinjiri ya ce ‘yan sandan da lamarin ya faru dasu a halin yanzu suna garkame kuma ana bincike a kan su.

Fustattun matasa sun kone motar 'yan sanda kurmus a Jigawa
Fustattun matasa sun kone motar 'yan sanda kurmus a Jigawa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Shagalin bikin Laolu Osinbajo, dan mataimakin shugaban kasa (Hotuna)

Wani ganau ba jiyau ba, Hamza Bello, ya sanar da kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa mutane takwas ne suka samu rauni yayin hatsarin.

“Wajen karfe 8 na daren ranar Juma’a ne motar sintiri ta bi wata mota kirar Golf da gudu a kan titin Hadejia zuwa UBA. Motar wacce ke dauke da buhunan masara da barkono ta fadi kusa da tashar mota ta Malammadori inda ta raunata mutane biyar da ke ciki tare da wasu ukun da ke kan babur a gefen titi,” ya ce.

A yayin martani a kan aukuwar lamarin, shugaban karamar hukumar, Bako Kashidila ya roki jama’ar yankin da su kwantar da hankulansu.

Kashidila ya ce za a tabbatar da cewa an binciki wannan gangancin tare da yin adalci ga iyalan mamaciyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel