Shagalin bikin Laolu Osinbajo, dan mataimakin shugaban kasa (Hotuna)

Shagalin bikin Laolu Osinbajo, dan mataimakin shugaban kasa (Hotuna)

- Dan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Laolu ya samu auren rabin ransa

- A cikin kwanakin nan ne Laolu ya samu damar auren rabin ransa a wani kayataccen biki da suka yi

- Matashin ya wallafa hotunan bikin gargajiyar da suka yi da matar shi mai suna Sekemioluwa Braithwaite

Biki ya kan kasance babban sha’ani a yankuna da yawa na duniya, ballantana a Najeriya. Ba kasafai ake ganin biki wanda bai zama abin tunawa ba ga ‘yan uwa da abokan arziki ko kuma ga ango da amaryar ba.

Abubuwa da yawa ne ke sa biki ya zama abin tunawa a zukatan jama’a. Daga kan shigar ango da amaryar zuwa kan ankon. Abincin da ake ci a wajen da kuma kyautukan da ake ba masu halartar bikin duk abin tunawa ne.

Wannan kuwa ya kasance abin tunawa da kuma murna ga dan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Laolu. Ya samu damar auren masoyiyarsa kuma rabin ransa.

DUBA WANNAN: Dan ta'addanci ya kai hari Masallaci a London, ya yanka wuyan Ladani (Hoto)

Laolu wanda ya bayyana a mai tsananin kaunar matar shi, ya wallafa haotunan su a kafar sada zumunta zamani ta Instagram.

Kyakyawwan angon ya saka babbar riga mai launi kore haka itama matar tashi ta saka kaya ne masu launin nashi.

A yayin wallafa hotunan, Laolu ya rubuta: “Sekemioluwa Osinbajo, kyakyawar matata. Nagodewa Ubangiji da ya bamu damar samun juna. Don haka zan daga hannu in yi addu’a da sunan Ubangiji. Ina matukar godiya gareka.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel