Cikawa mai kyau: Dattijo dan shekara 71 ya rasu yana sallar Juma’a a jahar Sakkwato
Malam Ahmad Muhammad, wani mazaunin garin Sakkwato mai shekaru 71 a rayuwa ya yi kyakkyawar karshe bayan ya rasu yayin da ake tsaka da gudanar da Sallar Juma’a a babban masallacin Sultan Bello dake jahar Sakkwato.
Daily Trust ta ruwaito wasu masallata dake sahu daya da Malam Ahmad sun bayyana cewa bayan an dago daga sujjada a raka’a ta biyu ne sai suka ga Ahmad ya gagara dagowa, jim kadan kuma sai ya tuntsire, shike nan rai ya yi halinsa.
KU KARANTA: An yi artabu tsakanin Yansanda da yan fashi a Abuja, 2 sun bakunci lahira
Jama’a da dama da suka san shi Ahmad sun bayyana shi a matsayin mutumin kirki, mai tsoron Allah, mai riko da addini, mai yawan fara’a da jama’a, mai saukin kai, kuma wanda jama’a suke ganin girmansa a unguwarsu.
Wasu jama’a kuma sun bayyana kaduwarsu da mutuwarsa sakamakon yan mintuna kadan kafin rasuwar tasa sai da ya yi wasan barkwanci da wasu, kuma lafiyarsa kalau don kuwa har ziyarar ta’aziyya ya kai ma wasu yan uwansa dake Filin Magaji a ranar Juma’ar.
Wani makwabcinsa mai ya shaida cewa: “Da misalin karfe 9 na safe na gan shi a gaban wani shago yana sayen rezar askin gashi a shirinsa na sallar Juma’a, daidai zai bar shagon sai ya hadu da wani abokinsa da yace sai ya riga shi zuwa Masallaci, sai Ahmad yace masa ‘Da ikon Allah sai na rigaka isa Masallaci’
Uwargidar Ahmad, Malam Halima mai shekaru 58 wanda suka kwashe shekaru 34 tare, inda suka haifi yara 3, Saudatu, Zara’u da Abubakar ta bayyana shi a matsayin mutumin kirki mai dattaku.
“Tare da jikokinmu ya tafi Masallacin Juma’a, wannan shi ne haduwata da shi ta karshe. A tsawon shekaru 34 da muka kwashe, bamu taba fada da shi ba, shi ne rayuwata.” Inji ta.
A wani labarin kuma, Mai alfarma Sarkin Musulmi, kuma shugaban majalisar koli ta Musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya baiwa yan Najeriya tabbacin Najeriya za ta samu nasara a yakin da take yi da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram duk da halin da ake ciki.
Sultan ya bayyana haka ne a babban birnin tarayya Abuja yayin taron kasa da kasa a kan soyayya da zaman tare karo na 5, wanda aka yi ma taken “Yaki da zafin ra’ayi don samar da zaman lafiya” da gidauniyar UFUK Dialogue ta shirya.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng