An bankado shirin ISIS na kai hari wani babban coci a Ingila - in ji ɗan kunan bakin wake

An bankado shirin ISIS na kai hari wani babban coci a Ingila - in ji ɗan kunan bakin wake

A ranar Juma'a ne wata mata mai shekaru 36 da ta dau alkawarin biyayya ga kungiyar 'yan ta'adda mai suna Islamic State ta musanta zargin da ake mata. Ana zargin matar ne da yunkurin dasa bam a cocin St Paul da ke London tare da wani otal mai kusanci da shi.

Safiyya Amira Shaikh ta musanta laifin da ake zarginta da shi a gaban kotun laifuka ta London wacce aka fi sani da 'Old Bailey'.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, za a yanke mata hukunci ne a ranar 11 ga watan Mayu mai zuwa sakamakon aikin ta'addancin da tayi da kuma watsa wallafe-wallafe na ta'addanci.

ISIS na shirin kai hari wani babban coci a Ingila - in ji ɗan kunan bakin wake
ISIS na shirin kai hari wani babban coci a Ingila - in ji ɗan kunan bakin wake
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Barkewar sabuwar cuta a Benue: 'Yan majalisa sun bukaci a kebance dan majalisa mai wakiltar yankin

Shaikh dai an kama ta ne bayan da aka ji tana tattauna shirinta na kai hari tare da dasa wasu abubuwa biyu masu fashewa. Jami'an tsaron farin kaya ne suka bankado shirinta.

Jami'an 'yan sandan cikin birnin London din sun ce ta binciki yadda za ta kai hari ne kuma ta kammala shirinta na aiwatarwa. Daga nan ta tafi London inda ta kama dakin otal don kammala aiwatar da manufarta.

Shaikh ta ba wa dan sandan farin kaya jakunkuna biyu wanda taso a cika mata da abubuwa masu fashewa sannan ta bayyana masa cewa ta dau rantsuwar kungiyar ta'addancin nan ta Islamic State.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel