Bayan kwashe watanni ana shari’a, an yankewa Rashidah da ta kashe mijinta a Kano hukuncin kisa

Bayan kwashe watanni ana shari’a, an yankewa Rashidah da ta kashe mijinta a Kano hukuncin kisa

Wata babbar kotun jihar Kano a ranar Jumaa ta yankewa wata mata mai suna Rashida Saidu hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin kisan mijinta, Adammu Ali, ta hanyar turoshi daga gidan tsauni a jihar.

An shigar da Rashida kara kotu ne a shekarar 2019 kan zargin ta nada hannu cikin kisar mijinta wanda ya kasance ma’aikaci a kwalejin ilimin tarayya FCE Kano.

Lauyan gwamna, Mariam Jibrin, ta bayyana kotu cewa Rashida ta samu sabani da mijinta ne a gidansu dake unguwar Dorayi kimanin shekara daya da ta gabata.

Ta kara da cewa yayinda suka fara fada, sai ta turoshi kasa daga gidan tsauni kuma hakan yayi sanadiyar mutuwarsa.

Yayinda ake shari’ar, an gabatar da shaidu hudu a kotun domin bayar da shaida kan tuhumar da ake mata.

Amma Rashida ta bakin lauyanta, Iliya Dauda, ta musanta zargin kuma ya gabatar da nata shaidun.

Bayan kwashe watanni ana shari’a, an yankewa Rashidah da ta kashe mijinta a Kano hukuncin kisa
Bayan kwashe watanni ana shari’a, an yankewa Rashidah da ta kashe mijinta a Kano hukuncin kisa
Asali: Twitter

A bangare guda, Maryam Sanda ta bayyana rashin amincewarta da hukuncin kisan da babbar kotun tarayya Abuja ta yanke mata kuma ta daukaka kara zuwa kotun daukaka kara dake Abuja.

A ranar 27 ga watan Janairu ne mai sharia Yusuf Halilu ya yanke ma Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ya kamata da laifin kashe mijinta Bilyaminu Muhammad Bello, sai dai Maryam ta bayyana hukuncin a matsayin wanda ke cike da son kai da rashin adalci.

Maryam ta ce kotun ta hanata daman sauraronta, sa’annan ta yanke mata hukunci a kan wasu hujjoji marasa kwari duk da cewa shaidun da aka gabatar basu da tabbaci, kuma babu wanda ya bayyana makamin da ake zargin ta yi amfani da shi, balle kuma rahoton binciken gawa da zai tabbatar da abin da ya kashe mijin nata.

Cikin karar da ta daukaka, Maryam Sanda ta hannun lauyoyinta Rickey Tarfa, SAN, Olusegun Jolaawo, SAN, Regina Okotie-Eboh da Beatrice Tarfa ta bayyana hukuncin babbar kotun a matsayin barin sharia, sa’annan ta yi zargin Alkalin bai bata daman bayar da jawabinta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel