Da duminsa: Sojoji na artabu da yan Boko Haram yanzu haka a Yobe

Da duminsa: Sojoji na artabu da yan Boko Haram yanzu haka a Yobe

Jaruman Sojojin Najeriya suna musayar wuta yanzu haka da yan taaddan Boko Haram a kauyen Latawa, karamar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe.

Mutan garin sun arce daga muhallansu gudun tsallen harsasai.

Mataimakin diraktan yada labaran rundunar Sakta 2 na Operation Lafiya Dole, Laftanan Chinonso Oteh, ya bayyanawa Channels TV cea an tura Sojoji wajen kuma babu tabbacin cewa sun yi garkuwa da fasinjoji.

A baya Mun kawo muku rahoton cewa Yan taa’ddan Boko Haram sun kai hari yanzu a garin Korongilum dake karamar hukumar Chibok ta jihar Borno a ranar Talata.

Wani jarumin jami’in soja ya rasa kafarsa yayinda aka nemi abokan aikinsa biyu aka rasa yayinda suka taka Bam da wasu yan Boko Haram suka dasa a Korongilum.

An tura Sojoji garin ne da safiyar ranar Laraba domin kawar da yan Boko Haram da suka garin daren Talata.

Majiyoyi daga gidan Soja sun bayyanawa manema labarai ranar Alhamis cewa rundunar 117 Bataliya dake Chibok sun kusa isa garin Korongilum yayinda Bam ya tashi da motocin da suka dauke da su.

“Sojoji bakwai sunyi matukar jikkata, kuma daya daga cikinsu ya rasa kafarsa“

“Kwamandan bataliyan, Laftanan Kanar SA Yahaya ne ya jagoranci tawagar. Da alamun shi aka nufa da Bam din amma ba ya cikin motar lokacin.“ cewar majiya

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel