Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda

Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda

Kamar yadda muka saba, mu kan kawo muku shawararin da zasu inganta kiwon lafiyar mabiyanmu saboda rai da lafiya ne ginshikin rayuwar dan Adam.

Kodarmu na daya daga cikin abubuwa masu matukar muhimmanci a jikin dan Adam wanda rashinsa babban barazana ne ga ran dan Adam.

Koda ke aikin tace abubuwa maras amfani da muka sanya cikinmu, koda ke samar da fitsari, rage hawar jini da sauransu.

A cewar masana kiwon lafiya, ciwon siga da hawar jini ne manyan cututtukan da ke lalata kodar dan Adam.

Ga abubuwa 7 da ka iya lalata kodar mutun idan sukayi yawa a jiki

1. Jan nama - Jan nama na dauke da kwayoyin gina jiki wato Protein da yawan gaske. Duk da cewa jiki na bukatar wannan domin gina jiki, yawan Protein a jiki na wahalar da kodar wanda zai sa shi gajiya da wuri.

Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda
Jar Nama
Asali: Facebook

2. Man Shanu - Man Shanu na dauke da mai wanda ka iya haddasa ciwon zuciya. Gidauniyar Koda ta kasa ta bayyana cewa ciwon zuciya babban barazana ne ga lafiyar koda

Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda
Man shanu
Asali: Facebook

3. Gyada - Gyada na dauke da sinadarin Oxalate, shi ke haddasa duwatsun da ke tsirowa idan koda ya kusa lalacewa

Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda
Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda
Asali: Facebook

4. Giya da kayan maye - Giya da barasa na daya daga cikin abubuwan da ke saurin lalata kodar dan Adam saboda ta kan sauya yanayin jikin mutum cikin kankanin lokaci.

Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda
Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda
Asali: Facebook

5. Gishiri - Asali, gishiri na da amfani da jikin dan Adam. Yana rage hawan jini, yana tafiyar da ruwan jiki, kuma yana taimakawa jijiyoyin. Amma idan yayi yawa, zai iya lalata kodar mutum.

Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda
Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda
Asali: Facebook

6. Lemun kwalba mai gas - Lemun kwalban da aka cushe da iskar gas. Yawan shan su na iya ynjo tsirar duwatsu da kodar dan Adam.

Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda
Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda
Asali: Facebook

7. Shan sigari - Yawan shan sigari na da matukar hadari ga jikin dan Adam. Sigari daya kacal na dauke da kimanin sinadarai 4800, 69 daga cikin shahrarrun masu sabbaba ciwon daji ne.

Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda
Kiwon lafiya: Abubuwa 7 da ka iya lalata maka koda
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel