Da duminsa Jam'iyyar APC ta bukaci kotun koli ta sake duba shariar jihar Bayelsa

Da duminsa Jam'iyyar APC ta bukaci kotun koli ta sake duba shariar jihar Bayelsa

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta garzaya kotun koli inda ta bukaci kotun ta janye shari'arta kan zaben gwamnan jihar Bayelsa da ta yanke ranar Alhamis da ta gabata.

A karar da lauyan APC, Wole Olanipekun SAN ya shigar madadin jamiyyar ya bukaci kotun ta sake duba shariar da ta yanke na soke zaben dan takarar gwamnan jihar, David Lyon, da mataimakinsa, Degi Biobarakuma.

Hakazalika ya bukaci kotun kolin ta soke tafsirin kuskure da hukumar gudanar da zabe ta kasa INEC ta yiwa shariar da kotun ta yanke ranar 13 ga Febrairu, 2020.

A yanzu dai kotun bata sa ranar sauraron karar ba.

Da duminsa Jam'iyyar APC ta bukaci kotun koli ta sake duba shariar jihar Bayelsa
Da duminsa Jam'iyyar APC ta bukaci kotun koli ta sake duba shariar jihar Bayelsa
Asali: Depositphotos

Zaku tuna cewa Ana saura awanni kasa da 24 da rantsar da sabon gwamna, kotun koli ta fitittiki David Lyon a matsayin zababben gwamnan jihar Bayelsa tare da mataimakinsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo matsayin wadanda suka lashe zaben 16 ga Nuwamba 2019.

Alkali Ejembi Eko, wanda ya karanto da shari'ar ya yi amfani da shari'ar babbar kotun tarayya dake Abuja da ta hana Degi-Eremiwoyo takara a zaben gwamnan.

Kotun kolin ta tabbatar da shari'ar karamar kotun cewa zababben mataimakin gwamnan ya aikata laifi wajen gabatar da kwalin bogi ga hukumar INEC.

Kwamitin Alkalan kotun koli kan karar karkashin jagorancin, Mary Odili, sun yi ittifakin cewa mutum bai cancanci takara a zabe ba muddin ya gabatar da takardun boge domin zaben.

Jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta shigar da kara kotu kan zargin gabatar da takardun boge da take yiwa dan takarar kujerar mataimakin gwamnan APC, Degi-Eremienyo.

Sun tuhumceshi da gabatar da sunayen daban-daban guda biyar matsayin sunayensa cikin kwalayen karatunsa.

PDP ta ce sunan zababben mataimakin gwamnan dake cikin kwlain karatun firamarensa ya banbanta da na sakandare hakazalika na jami'a.

Ga jerin yadda sunayensa sukea kwalayen:

Kwalin karatun Firamare - Degi Biobara

Kwalin karatun Firamare - Adegi Biobarakumo

Kwalin karatun Jami'a- Degi Biobarakuma

Kwalin karatun Jami'a MBA - Degi Biobarakuma Wangaha

Sunansa a zaben 2019 - Degi-Eremienyo Biobarakuma

Wannan shine dalilin da ya sa kotun koli ta fitittiki zababben gwamnan da mataimakinsa saboda tikitin da sukayi takara daya ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel