Hukuncin kisa: Maryam Sanda ta kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara

Hukuncin kisa: Maryam Sanda ta kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara

Biyo bayan kama ta da laifi, tare da yanke mata hukuncin kisa da wata babbar kotun tarayya dake babban birnin Abuja ta yi, Maryam Sanda ta bayyana rashin amincewarta da hukuncin, kuma ta daukaka kara zuwa kotun daukaka kara dake Abuja.

A ranar 27 ga watan Janairu ne mai sharia Yusuf Halilu ya yanke ma Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ya kamata da laifin kashe mijinta Bilyaminu Muhammad Bello, sai dai Maryam ta bayyana hukuncin a matsayin wanda ke cike da son kai da rashin adalci.

KU KARANTA: Yan sa kai a jahar Borno sun mayar ma Shekau martani cikin sabon bidiyo

Maryam ta ce kotun ta hanata daman sauraronta, sa’annan ta yanke mata hukunci a kan wasu hujjoji marasa kwari duk da cewa shaidun da aka gabatar basu da tabbaci, kuma babu wanda ya bayyana makamin da ake zargin ta yi amfani da shi, balle kuma rahoton binciken gawa da zai tabbatar da abin da ya kashe mijin nata.

Cikin karar da ta daukaka, Maryam Sanda ta hannun lauyoyinta Rickey Tarfa, SAN, Olusegun Jolaawo, SAN, Regina Okotie-Eboh da Beatrice Tarfa ta bayyana hukuncin babbar kotun a matsayin barin sharia, sa’annan ta yi zargin Alkalin bai bata daman bayar da jawabinta ba.

“Alkalin kotun ya tafka kuskure bayan ya saurari wanda ake kara lokacin da ta musanta tuhume tuhumen da ake mata a ranar 19 ga watan Maris, amma bai yanke hukunci a kan hakan ba har aka kammala shari’ar.

“Alkalin ya nuna son kai ta hanyar rashin yanke hukunci a kan kalubalantar huruminsa na sauraron karar da wanda ake kara ta yi, wanda hakan ya saba ma yancin sauraron wanda ake kara.” Inji lauyoyinta.

Bugu da kari Maryam ta kalubalanci hukuncin bisa cewa Alkali Halilu ya daura ma kansa aikin Dansanda a yayin shari’ar kamar yadda ya bayyana a shafi na 76 na hukuncin da ya yanke, haka zalika hujjar daya dogara da ita na cewa Maryam ce wanda ta ga mijinta na karshe a lokacin bai isa ya tabbatar da ita ta kashe shi ba.

Da wannan ne Maryam ta ke rokon kotun daukaka kara ta amince da bukatunta, ta soke hukuncin babbar kotu, sa’annan ta wanketa daga tuhumar da ake mata. Sai dai kotun ba ta sanya ranar fara sauraron karar ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng