Yau watanni biyu kenan, gwamnan Taraba ya tare a Abuja bai taka jiharsa ba

Yau watanni biyu kenan, gwamnan Taraba ya tare a Abuja bai taka jiharsa ba

Yau watanni biyu cir rabon da gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya taka jiharsa ba kuma mutan jihar sunce yanayin gudanar da aikin gwamnatin jihar Taraba ya ja tsaya cik saboda rashin gwamnan, Rahoton Daily Trust.

Aikin shi na karshe kafin barin jihar shine gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar dokokin jihar a ranar 19 ga watan Disamba 2019.

Jim kadan bayan gabatarwar, aka samu rahoton cewa ya bar Jalingo a ranar 22 ga watan Disamba 2019 kuma tun daga nan ba’a sake ganin kafarsa ba.

Gwamnan bai bar wa mataimakinsa, Alhaji Haruna Manu, rikon kwarya ba, sannan bai sanarwa yan majalisar jihar ba.

KU KARANTA: EFCC ta damke dan tsohon gwamna, Abubakar Audu

Bincike ya nuna cewa tun daga 19 ga watan disamba 2019 har yau, ba’a sake ganawar majalissar zantarwar jihar ba.

Har ila yau, ba wani aiki da yake gudana yanzu a Jalingo, mutane da yawa na jihar sun nuna damuwar su game da rashin gwamnan.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Barista Ibrahim EL-sudi, yace rashin gwamnan a jihar har na kimanin kwanaki 55 ba tare da wani dalili ko ba mataimakin shi rikon kwarya ba babban kuskure ne.

Yace “Bama cikin farin ciki saboda rashin gwamna domin akwai abubuwan da mataimakin shi ba zai iya yi ba idan baya nan, aiyuka da dama sun tsaya cak a jihar.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel