Ta bayyana: Yadda 'Yahoo boys' suka yiwa mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa mumunan kisa a Abuja

Ta bayyana: Yadda 'Yahoo boys' suka yiwa mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa mumunan kisa a Abuja

Bayanai sun kara bayyana kan sanadiyar mutuwar mataimakiyar darakta a fadar shugaban kasa Asp Villa wacce ta rasa ranta daren Litinin, 17 ga watan Febrairu a gidanta dake 22 Road C Close, Efab Estate, Lokogoma Abuja.

Naankang, mai kimanin shekaru 47, wacce wasu yan damfarar yanar gizo da akafi sani da suna “yahoo boys” suka kashe.

An samu rahoto cewa marigayiyar ta gano cewa a unguwar Lokogoma dake Abuja inda take zama cike take da ‘yahoo boys’ wadda ya haifar mata rashin natsuwa da wurin.

Hakan yasa ta fadawa kawayenta cewa zata bar unguwar sannan ta yanke shawarar sanar da jami’an tsaro gudun kar abin ya shafe ta.

Duk da haka, yan sandan da ta kaiwa kara maimakon su dauki kwakkwaren mataki, kawai sai suka saki wadanda ake zargin.

KU KARANTA Asiri ya tonu: An gano wuraren da ake boye shanun sata a Zamfara

Yan ta’addan sun daure tane a gidan ta inda take zama ita kadai, suka mata fyade suka shaketa har lahira sannan s

Ta bayyana: Yadda 'Yahoo boys' suka yiwa mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa mumunan kisa a Abuja
Latieltte Dagan
Asali: Facebook

uka banka mata wuta.

Bayan haka an samu rahoto cewa mai gadinta wanda ake zargin da sa hannunshi a wannan aika aika an damke shi, sannan an samu bayanai daga gare shi da zasu taimaka wurin gano yan ta’addan.

Har ila yau, daya daga cikin yan ta’addan ya bar wayar shi a wurin da abin ya faru

Marigayiyar, yar jihar Plateau, bisa ga wani bayani daga mataimakin daraktan sadarwa, Mr Attah Esa, cewa a ranar Talata, sun yi aiki a offishin nata a ranar litinin har 8:00pm sai kawai mutuwar ta suka ji wuraren 11:00pm ga wasu ya ta’adda.

Ana da yakinin cewa wayar zata taimakawa jami’an tsaron wajen gano yan ta’addan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel