Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa ta nemi a kafa hukuma domin tubabun 'yan Boko Haram

Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa ta nemi a kafa hukuma domin tubabun 'yan Boko Haram

Majalisar Dattawar Najeriya a ranar Alhamis ta gabatar da wani kudirin kafa hukuma ta musamman da za ta rika sauya wa tubabbun 'yan Boko Haram mummunan tunaninsu da koyar da su sana'o'i kafin daga baya a sake su su koma cikin al'umma.

Sanata Ibrahim Gaidam mai wakiltar Yobe ta Gabas ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisa kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa ta nemi a kafa hukuma ta musamman domin tubabun 'yan Boko Haram
Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa ta nemi a kafa hukuma ta musamman domin tubabun 'yan Boko Haram
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Asiri ya tonu: An gano wuraren da ake boye shanun sata a Zamfara

A baya rundunar sojojin Najeriya ta mika daruruwan tubabbun 'yan Boko Haram ga gwamnatin jihar Borno bayan ta sauya musu mugun tunaninsu.

Shugaban hafsoshin tsaron Najeriya, Abayomi Olonisakin ya ce tsarin na sauya wa tubabbun yan ta'addan mugun tunaninsu, wani bangare ne daga cikin operation Safe Corridor da aka shirya domin wadanda ke son ajiye makamansu su mika kai.

Ya ce, "tsarin zai taimaka musu su koma yadda suke rayuwa a baya. Kazalika, an kafa kwamiti da ta ƙunshi gwamnonin Adamawa, Borno, Yobe da shugabannin hukumomin tsaro a karkashin jagorancin sa."

Sai dai wasu daga cikin 'yan Najeriya sun soki shirin inda suka ce ba su gamsu cewa a riƙa sakin tubabbun yan ta'addan su koma cikin mutane ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164