An kama buhunan shinkafa 1,393 da aka boye cikin tukwanen iskar gas (Hotuna)

An kama buhunan shinkafa 1,393 da aka boye cikin tukwanen iskar gas (Hotuna)

Jami'an hukumar Kwastam ta Najeriya, NCS, sun kama buhunnan shinkafa 1,393 da aka boye a cikin tukwanen iskar gas ta girki a jihar Ogun.

Da ya ke holen masu shigo da shinkafar da barauniyar hanya ga manema labarai a ranar Laraba 19 ga watan Fabrairu, mukadashin kwantrola na sashin ayyuka, FOU, Zone A a Ikeja, Usman Yahaya ya ce an kuma kama katan din daskararrun kaji 625, jarka da gangunan man gyada 253 tare da kama wadanda ake zargi daga ranakun 5 zuwa 17 ga watan Fabrairun 2020.

Kayayyakin da aka shigo da su a motocci daban-daban an kiyasta cewa ya kamata a biya musu harajin kwastam ta Naira miliyan 40.14 kamar yadda Linda Ikeji Blog ta ruwaito.

An kama buhunan shinkafa 1,393 da aka boye cikin tukwanen iskar gas (Hotuna)
An kama buhunan shinkafa 1,393 da aka boye cikin tukwanen iskar gas (Hotuna)
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wutan lantarki ta kashe shugaban masu tsaron Rotimi Amaechi a Kaduna

An kama buhunan shinkafa 1,393 da aka boye cikin tukwanen iskar gas (Hotuna)
An kama buhunan shinkafa 1,393 da aka boye cikin tukwanen iskar gas (Hotuna)
Asali: Twitter

Yahaya ya ce, "Kimanin sati biyu bayan ziyarar aiki da shugaban kwastam ya kai Legas inda ya yi holen kayayyakin da aka kwace da darajar su ta dara Naira Biliyan 10, mun kuma sake kama buhunan shinkafa 1,393, jarkokin man gyada 187 da ganguna 66 da katon din kaji 625 da aka shigo da su ta haramtaciyyar hanya a jihar Ogun daga ranar 5 zuwa 17 na watan Fabrairu yayin sintiri.

"Yadda bata garin ke kokarin boye shinkafa cikinn tukunyar gas ya nuna cewa jami'an Kwastam na aiki sosai. Ga kudin harajin da ya kamata a biya wa wadannan kayayyakin kamar haka; Shinkafa, Naira miliyan 27.86, man gyada, Naira miliyan 6.28 da kaji Naira miliyan 6."

An kama buhunan shinkafa 1,393 da aka boye cikin tukwanen iskar gas (Hotuna)
An kama buhunan shinkafa 1,393 da aka boye cikin tukwanen iskar gas (Hotuna)
Asali: Twitter

Ya kuma bukaci mutane su cigaba da bawa jami'an hukumar hadin kai ta hanyar basu bayanai a kan wadanda ke safarar kaya da barauniyar hanya domin hukumar ta cigaba da taka wa mata garin birki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel