Bauchi: Dan sanda ya harbi mai babur domin ya hana shi cin hanci ta Naira 50

Bauchi: Dan sanda ya harbi mai babur domin ya hana shi cin hanci ta Naira 50

Wani jami'in dan sanda a karamar hukumar Ningi na jihar Bauchi ya harbi wani Sabo Idris da ke hanyarsa zuwa wurin hakar ma'adinai da ke Burra saboda ya ki bashi cin hanci na kudi Naira hamsin.

Kawun Sabo, Adamu Yakubu a hirar wayar tarho da Leadership ya yi ikirarin cewa dan sandan ya tsayar da wanda abin ya faru da shi ne yayin da suke sintiri kuma ya harbe shi a kafa saboda jayayya da suka yi a kan cin hanci ta Naira 50.

Adamu ya yi ikirarin cewa, "Suna hanyarsu ta zuwa wurin hakar ma'adinai ne, sun wuce shingen sojoji sai suka sake haduwa da 'yan sanda da ke sintiri amma da Sabo ya ki bawa 'yan sanda abin da suke nema na cin hanci, daya daga cikinsu ya harbe shi a kafa saboda ya yi yunkurin tafiya ba tare da ba su cin hancin Naira 50 ba."

Dan sanda ya harbi mai babur domin ya hana shi cin hanci ta Naira 50
Dan sanda ya harbi mai babur domin ya hana shi cin hanci ta Naira 50
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Wutan lantarki ta kashe shugaban masu tsaron Rotimi Amaechi a Kaduna

Ya kara da cewa, "Yan sandan su kan tsaya a wani wuri musamman a ranakun cin kasuwa domin su rika karbar cin hanci daga hannun mutane musamman fulani da ke wucewa a kan hanyar da baburansu a hanyar Ningi Burra.

"Bayan afkuwar lamarin, matasan unguwar sun fusata kuma sun nemi daukar doka a hannunsu amma hakimin Burra, Alhaji Ya'u Shehu da DPO Danladi Muhammad suka lallashe su kuma suka ce za a gudanar da bincike tare da hukunta wanda aka samu da laifi," in ji shi.

Adamu ya kara da cewa DPO na 'yan sanda da kansa ya dauki wanda aka harba ya kai shi babban asibitin Burra domin ayi masa magani.

Shaibu Mohammed Ningi, abokin Sabo da suke kan babur din tare lokacin da aka harbi Sabo ya ce, "abinda ya fi mana ciwo shine yanayin da DPO ya dauki lamarin, a maimakon ya nuna nadama da rashin jin dadin abinda dakarunsa suka aikata, yana zargin cewa gudu mu ke yi duk da cewa baya nan a lokacin da abin ya faru."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel