Gwamnan Kwara ya kori shugabannin gidajen watsa labarai 3 a jiharsa

Gwamnan Kwara ya kori shugabannin gidajen watsa labarai 3 a jiharsa

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrasaq ya amince da sallamar shugabannin gidajen watsa labarai na jihar guda uku.

Gidajen watsa labaran da lamarin ya shafa sun hada da gidan jarida na Herald, gidan rediyo na Kwara da gidajan talabijin na jihar ta Kwara.

Sanarwar da kwamishinan jihar na watsa labarai, Alhaji Muritala Olanrewaju ya raba wa manema labarai a ranar Laraba a Ilorin ta ce shugabanin gidajen watsa labaran su mika aiki ga direkta mafi girma a hukumominsu.

Gwamnan Kwara ya kori shugabannin gidajen watsa labarai 3 a jiharsa
Gwamnan Kwara ya kori shugabannin gidajen watsa labarai 3 a jiharsa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wutan lantarki ta kashe shugaban masu tsaron Rotimi Amaechi a Kaduna

Gwamna Abdulrazaq a cewar sanarwar ta gode wa tsaffin shugabannin kana ya bukaci "su mika aiki ga direktoci mafi girma a gidajen watsa labaran kafin lokacin da za a nada sabbin shugabanni."

Gidajen watsa labaran suna dab da rushewa ne a karshen wa'addin gwamnatin da ta gabata a jihar.

Sai dai sun fara aiki kuma bayan da gwamnati mai ci yanzu ta dare kan karagar mulki kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel