Miji ya bantarewa matarshi hakora guda 4 bayan ya gano 'ya'yansu uku da ya wahala yana raino ba nashi bane

Miji ya bantarewa matarshi hakora guda 4 bayan ya gano 'ya'yansu uku da ya wahala yana raino ba nashi bane

- Wata mata 'yar Najeriya ta shiga garari bayan da mijinta yayi mata mugun duka har da cire mata hakora hudu

- Asirin cin amanar shi da take yi ya tonu ne bayan da ya gano yaransu uku duk ba nashi bane

- A kokarin shi na komawa Canada da iyalanshi ne ofishin jakadanci ya bukaci gwajin kwayar halittar yaran don tabbatar da cewa nashi ne

Wata mata 'yar Najeriya na cikin tsananin radadin bakin ciki bayan ta rasa hakoranta hudu. Mijinta ne ya dinga dukanta bayan ya gano cin amanar shi da ta dinga yi.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, asirin matar ya tonu ne bayan da mijinta ya fara shirin komawarsu Canada. Tashin hankalin ya auku ne bayan da ofishin jakadanci suka bukaci gwajin kwayoyin halittar 'ya'yan shi don tabbatar da cewa nashi ne zai bar kasar tare dasu, kamar yadda jaridar Within Nigeria ta ruwaito.

Miji ya cirewa matarshi hakora guda 4 bayan ya gano 'ya'yansu uku da ya wahala yana raino ba nashi bane
Miji ya cirewa matarshi hakora guda 4 bayan ya gano 'ya'yansu uku da ya wahala yana raino ba nashi bane
Asali: Facebook

KU KARANTA: Mutane sun mutu yayin da jiragen sama suka yi taho mu gama a sararin samaniya

Mijin ya fusata bayan da gwajin ya nuna cewa yaran uku duk ba nashi bane.

Mijin ya garzaya gida don bukatar gamsassun bayanai a kan yadda ya dinga wahala a kan 'ya'yan da ba nashi ba tun haihuwarsu.

Bayan kasa amsa tambayoyin shi, mijin ya dinga dukanta har sai da ya cire mata hakora hudu.

Wata mata kuma da abin duniya ya isheta na irin cin zarafin ta da mijinta yake, fitowa tayi shafin Facebook ta bayyanawa duniya halin da take ciki.

Matar ta bayyana cewa tana so mutane su shaida, idan har aka ga gawarta to tabbas kada a zargi kowa, a zargi mijinta.

Ta kara da cewa bashi da aiki sai dukanta, saboda haka ita a yanzu haka ma ta gaji da auren, kuma tana fatan samun sauki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel