Kwankwaso ya yi kira ga kotun koli ta sake nazari game da shari’ar gwamnan Kano

Kwankwaso ya yi kira ga kotun koli ta sake nazari game da shari’ar gwamnan Kano

Tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga kotun kolin Najeriya da ta sake yin nazari tare da sake duba shari’ar gwamnan Kano da idon basira, wanda ta baiwa Abdullahi Umar Ganduje.

A watan da ta gabata ne kotun koli ta tabbatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin halastaccen gwamnan jahar Kano, kotun ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara ta yanke a kan sharia’ar, da ma kotun sauraron koke koken zabe.

KU KARANTA: Ta’addanci: Boko Haram ta kashe malaman makaranta 547 a yankin Arewa maso gabas

Kwankwaso ya yi wannan kira ne a ranar Laraba, 19 ga watan Feburairu yayin da ya jagoranci wata tawagar yayan jam’iyyar PDP daga jahar Kano zuwa sakatariyar jam’iyyar PDP dake Abuja, inda ya nemi goyon bayan uwar jam’’iyyar game da wannan bukata tasa.

Malam Ibrahim Ahmad, wanda shi ne mai magan da yawun tsohon dan takarar gwamnan jahar Kano a jam’iyyar PDP, Injiniya Abba Kabir Yusuf inkiya Abba Gida Gida ne ya bayyana haka, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

Ahmad yace Kwankwaso ya koka kan yadda aka yi ma al’mmar jahar Kano fashi ta hanyar magudin zabe da kuma murdiya daga fannin sharia, don haka ya nemi PDP ta shiga cikin maganan don ganin kotun koli ta duba bukatarsu.

A jawabinsa, shugaban PDP, Uche Secondus, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban PDP, Suleiman Nazif ya bayyana cewa jam’iyyar PDP na kallon jahar Kano a matsayin matattarar masoyanta, don haka za ta yi duk mai yiwuwa don kare muradunta a jahar.

Nazif ya yaba ma Kwankwaso dangane da yadda ya jagoranci jam’iyyar zuwa ga nasara a zaben 2019, amma wasu suka hada baki wajen yi ma nasarar jam’iyyar PDP zagon kasa.

Daga karshe ya jinjina ma kokarin da Kwankwaso yake yi wajen daukan nauyin matasa zuwa kasashen waje don yin karatu, inda yace wannan ne karo na farko da ake samun wani mutum da baya rike da mukamin siyasa yake wannan aiki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel