Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Alli Sarumi ya rasu

Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Alli Sarumi ya rasu

Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Alli Sarumi ya rasu.

Mista Sarumi da ake yi wa lakabi da "Alli Bay" a lokacin da ya ke kuruciyar siyarsa ya rasu ne cikin barcinsa a ranar safiyar Talata a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Ya rasu yana da shekaru 81 a duniya.

Tuni an yi jana'izarsa bisa koyarwan addinin musulunci a gidansa da ke Bashorun Ibadan a ranar Talata.

Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Alli Sarumi ya rasu
Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya, Alli Sarumi ya rasu
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matawalle ya dauki mataki kan hukuncin kisa da Saudiyya ta yanke wa Malamin Najeriya

Daya daga cikin diyarsa, Bolanle Sarumi Aliyu ta tabbatar da rasuwar dan siyasar kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Bolanle wacce ta yi takarar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar National Interest Party (NIP) a zaben 2019 a jihar Oyo ta kara da cewa an yi wa mahaifinta jana'iza irin ta musulunci.

Alli Bay ya wakilci mazabar Ibadan ta Arewa a majalisar wakilai na tarayya daga 1999 zuwa 2003 a karkashin jam'iyyar Alliance For Democracy.

A cikin sanarwar da ta fitar, Bolanle Sarumi ta ce marigayin ya rasu ya bar 'ya'ya 10 da jikoki 20.

Za ayi addu'an Fidau a ranar 25 ga watan Fabrairu a gida mai lamba 3 Omo Oyin Way, Orita Bashorun a garin Ibadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel