'Yan uwa ku shaida, idan na mutu mijina ne ya kashe ni - Mata ta bar wasiyya

'Yan uwa ku shaida, idan na mutu mijina ne ya kashe ni - Mata ta bar wasiyya

- Wata mata da har yanzu take da ranta da lafiya kuma, ta bayar da wasiyya ga 'yan uwanta da abokanan arziki

- Matar ta sanar da 'yan uwan nata cewa idan har suka ji an ce ta mutu, to tabbas mijinta ne ya kashe ta

- Ta bayyana cewa ba sau daya ba ba sau biyu ba mijin nata na yawan yi mata barazana da rayuwarta, inda take ganin ba zata iya cigaba da zama da shi ba

Wata mata mai koyar da yadda ake dafa abinci mai suna Oluwabusayo Reuben, ta baiwa abokanan ta mamaki, bayan ta wallafa wani rubutu a shafinta na Facebook da take zargin mijinta mai suna Gbadebo da cin zarafinta.

"Lokaci yayi da duniya za ta san halin da nake ciki, ko bayan raina ku sani cewa ba kowane ya kashe ni ba face mijina.

"Ba mutumin arziki bane, abu kalilan idan ya hadamu sai ya hauni da duka, na gaji da auren daga yanzu, kuma ina so kowa ya san da wannan zancen.

'Yan uwa ku shaida, idan na mutu mijina ne ya kashe ni - Mata ta bar wasiyya
'Yan uwa ku shaida, idan na mutu mijina ne ya kashe ni - Mata ta bar wasiyya
Asali: Facebook

"Na fito daga bayi yau da dare, sai ya hauni da duka, har da gwara kai na a jikin bango, kiris ya rage ya shake mini wuya ya karni lahira, kawai saboda na hana shi kudi.

"Ina so duka dangin mu su san halin da nake ciki, hadda nashi dangin, duniya gabaki daya ta sani, hakuri na ya kare gaskiya.

Ta cigaba da cewa: "Anyi na farko anyi na karshe, na jure wannan wahalar tsawon shekaru biyar yanzu kenan."

KU KARANTA:

A wani labari da muka kawo muku kuwa, ita kuma budurwar ce ta sayar da motar da saurayinta ya siya mata sukutum saboda tsananin kaunar da yake yi mata.

Ta sayar da motar ne tayi amfani da kudin wajen sayan kayan auren wani sabon saurayi da tayi, ma'ana dai ta yaudari wancan da ya saya mata motar,

Ana ta faman samun rikici tsakanin ma'aurata da yake kai ga daya daga cikinsu ya dauki makami ya kashe daya, duk kuwa da hukuncin da hukuma ke dauka a kansu hakan bai sanya sun saduda ba.

'Yan uwa ku shaida, idan na mutu mijina ne ya kashe ni - Mata ta bar wasiyya
'Yan uwa ku shaida, idan na mutu mijina ne ya kashe ni - Mata ta bar wasiyya
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel