Kyau na bai amfana mini komai ba, saboda har yanzu bani da masoyi - Budurwa ta koka

Kyau na bai amfana mini komai ba, saboda har yanzu bani da masoyi - Budurwa ta koka

- Maza da yawa na nan a makale a gefe suna neman mace wacce take da dan karen kyau domin suyi soyayya da ita wasu ma har ta kai su ga aure

- To sai dai wani abin mamaki shine, yadda muka ci karo da wani labari a shafin sada zumunta na wata budurwa

- Budurwar ta bayyana cewa ita kuma maimakon kyawun nata ya jawo mata masoya sai ya zama yana korar masoyan nata, har ta kai ga ta fara kokawa akan lamarin

Budurwa ta shiga damuwa matuka, akan yadda samari ke gudunta maimakon su dinga rububin zuwa wajenta.

Budurwar mai suna Hauwa tace ta rasa dalilin da ya sanya mazan suke ta faman gudunta saboda tsananin kyawun da Allah yayi mata.

A wani rubutu da ta wallafa da yake ta faman yawo a shafukan sada zumunta, kyakkyawar budurwar ta bayyana rashin jin dadinta akan kyawun da take dashi, inda tace shine babban dalilin da ya sanya har yanzu bata da saurayi.

Kyau na bai amfana mini komai ba, saboda har yanzu bani da masoyi - Budurwa ta koka
Kyau na bai amfana mini komai ba, saboda har yanzu bani da masoyi - Budurwa ta koka
Asali: Facebook

Ta ce a lokuta da dama samari sukan turo mata sako na cewa suna sonta, kuma zasu kari rayuwarsu da ita, amma da abu yayi nisa sai su gudu, baza ta kara ji daga garesu ba.

"Sun ce kyauna yana basu tsoro, saboda wani namijin kan iya zuwa ya dauke ni, kuma hakan ya sanya basa jin za su iya cigaba da soyayya dani," Hauwa ta wallafa.

KU KARANTA: Cin amana: Budurwa ta sayar da motar da saurayinta ya bata kyauta ta yi shirin auren wani da kudin

"Dana fara girma, mutane suna matukar sona, kuma suna kula dani sosai, har ya sanya ni jin dadi cewa ina da matukar masoya, amma dana cika 'ya mace, sai na gano cewa kyau na bashi da wani amfani," cewar Hauwa.

"Ina ji ina gani kawayena suke yin aure, amma ni hakan ya gagara. Maza ko da yaushe suna nesanta kansu dani, suna cewa kyauna yayi yawa, inda suke cewa sun tabbata suna ji suna gani wani zai zo ya kwace ni, saboda sun tabbata idon mutane da yawa yana kaina, saboda haka da wuri za a iya kwace ni. Sunana Hauwa, daga jihar Adamawa, ni kuma Bafulatana ce," ta rubuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel