Zulum ya ziyarci Rann, ya rabawa iyalai 10,000 milyan dari

Zulum ya ziyarci Rann, ya rabawa iyalai 10,000 milyan dari

A ranar Talata, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci al'ummar Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala-Balge ta jihar Borno.

Wannan shine karo na uku da gwamnan zai kai ziyara tun lokacin da ya hau mulki.

Gwamnan ya rabawa gidajen mutane 10,000 da ambaliyan rafi ya hanasu iya fita daga garin milyan dari.

A jawabin da ofishin gwamnan ta saki, an bayyana yadda giwaye suka lalata amfani gonan da al'ummar Rann suka shuka a Disamban 2019.

Yace: "Kimanin iyalai 10,000 a garin Rann suna turke yayinda kimanin giwaye 250 suka lalata amfani gonan da suka shuka bisa rahoton majalisar dinkin duniya a Disamban 2019."

"Karkashin jagoranicn gwamna Zulum, jami'an gwamnati sun raba kudi N100m ga mazauna garin Rann wadanda mafita daya kacal da ya rage musu shine takawa kilomita 10 domin sayan kayayyakin masarufi."

DUBA NAN: Buhari ba zai kori su Buratai ba - Sakataran gwamnatin tarayya

"Kowani gida cikin 10,000 sun samu N10,000 da N15,000. Saboda rashin bankuna a wajen, sai da Zulum ya debi makudan kudi cikin jirgin sama."

"Yayinda mazaje suka samu N14,000, iyalansu mata sun samu N10,000."

"Ba su iya noma saboda ambaliya ya mamaye gonakinsu saboda haka hanyar rayuwa daya da suke da shi shine tallafin gwamnati."

A watan Junairun 2017, hukumar Sojin Operation Lafiya Dole sun yi kuskuren kashe kimanin masu farin hula 100 a sansanin IDP dake Rann inda sukayi tunanin yan Boko Haram ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel