Buhari ba zai kori su Buratai ba - Sakataran gwamnatin tarayya

Buhari ba zai kori su Buratai ba - Sakataran gwamnatin tarayya

A ranar Talata, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana cewa koran manyan hafsoshin tsaro a yanzu na da hadari ga lamarin tsaron Najeriya.

Mun kawo muku a baya cewa kungiyoyi daban-daban a fadin tarayya da masu sharhi kan lamuran yau da kullum basu gushe ba suna kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya sallami hafsoshin tsaro saboda sun yi kasa a gwiwa.

Hare-haren yan bindiga da garkuwa da mutane a Arewa maso yamma ya karu yayinda yan taaddan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso gabas suka addabi alummar Arewa maso gabas ba dare, ba rana.

Hari mafi muni na karshe da suka kai shine a garin Auno, hanyar Maiduguri zuwa Damaturu inda suka kashe akalla mutane 30 kuma suka lalata dukiyoyin miliyoyin naira.

Dukkan hafsoshin tsaron sun wuce shekaru hudu da doka ta tsara ga Soja yayi a sabis. Sun hada da Janar Abayomi Olonishakin (Babban hafsan tsaro), Laftanan Janar Tukur Buratai (Shugaban sojojin kasa), Air Marshal Sadique Abubakar (Shugaban mayakan sama) da Vice Admiral Ibok Atas (shugaban sojin ruwa).

Amma Shugaba Buhari da mukarrabansa sun lashi takobin cewa sam ba zasu sallami hafsoshin tsaron ba.

Boss Mustapha yace: "Ba haka ake koran mutane ba. Akwai hanyoyin da ake bi kuma na san idan lokacin yin hakan ya yi, za'a bi hanyoyin."

"Muna cikin wani hali mai wuya. Muna bukatan hadin kai tsakanin hukumomin tsaro domin kawar da wannan yaki."

"Amma idan muka fara kawo rabuwar kai, wa zai amfana da hakan? Wadanda ke ihun a canza ne kadai zasu amfana da lalacin kuma kasar zata cigaba da tabarbarewa."

Bayan haka, Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya yi bayani ranar Lahadi cewa ba cire hafsoshin tsaro magance matsalar tsaron da Najeriya ke fama da shi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel