An kama 'yan fashi da makami 5 a gidan boka

An kama 'yan fashi da makami 5 a gidan boka

Yan sandan jihar Ogun sun kama wasu mutane biyar da ake zargin masu fashi da makami ne da suka boye a gidan wani boka bayan sun aikata fashi da makami.

An kama wadanda ake zargin yan fashin ne a ranar Talata bayan sun kai hari a rikunin gidajen Akorede, Olomoore kusa da Jami'ar Crescent a Abeokuta a ranar 21 ga watan Janairun 2020.

Mai magana da yawun 'yan sandan, Abimbola Oyeyemi cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ya ce wadanda ake zargin 'yan fashin sun hada da Tosin Adebanjo, Toheeb Ogundare, Ahmed Oloyede, Emmanuel Ogunshina, da aka fi sani da Emma SARS, Adebisi Remilekun da Sukanmi Ogundimu (bokan).

Oyeyemi ya ce wadanda ake zargin sun yi wa wani Alfa Rifhat Ashraf rauni yayin da suka kai masa hari da tsakar dare.

Ya kara da cewa mutanen sun kuma kwace wa mutumin da matarsa kudi N60,000, wayoyin salula biyar, komfuta da wasu kayayykin masu muhimmaci.

An kama 'yan fashi da makami 5 a gidan boka
An kama 'yan fashi da makami 5 a gidan boka
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Matawalle ya dauki mataki kan hukuncin kisa da Saudiyya ta yanke wa Malamin Najeriya

Kakakin 'yan sandan ya ce, "Bayan sun samu rahoton, kwamishinan 'yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson ya bawa DPO na Lafenwa, CSP Muraina Ayilara umurnin ya kamo miyagun domin su fuskanci shari'a.

"Daya daga cikin 'yan tawagar masu fashi da makamin da aka kama ne ya yi wa yan sanda jagora zuwa unguwar Olomoore a Abeokuta inda yan tawagara ke buya.

"Bayan isarsu gidan 'yan sandan sun zagaye gidan. Miyagun sun kai wa yan sanda hari da adduna inda har yan sandan suka harbe daya daga cikinsu kuma suka kama guda biyar tare da boka.

"An kwato kwamfuta day, wayoyin salula daban-daban da adda da layu.

"Shugaban tawagar yan fashin da aka fi sani da AK ya tsere da munanan rauni kuma tuni an fara bin sahunsa domin a kama shi.

"Mutanen da aka yi wa fashi sun fara gane wasu daga cikin wadanda ake zargin a matsayin wadanda suka musu fashi a gidajensu a ranar."

Kwamishinan yan sanda, CP Keneth Ebrimson ya bayar da umurnin mika wadanda ake zargin zuwa sashin binciken masu yaki da fashi da makami domin zurafafa bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel