Tashin hankali: An gano bindigu kirar AK-47 da alburusai a siddin babur (Bidiyo)

Tashin hankali: An gano bindigu kirar AK-47 da alburusai a siddin babur (Bidiyo)

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi holen wani mutum da ake zargin yana cikin kungiyar 'yan bindiga da suka saba kai hare-hare ne a kauyukan da ke arewacin Najeriya tare da bindigu AK-47 biyu da alburusai da aka samu a karkashin kujerar babur dinsa.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Najeriya, Frank Mba da ya bayyana kamen a matsayin 'abu mai ban mamaki' ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan gudanar da binciken kwaf-kwaf.

Ya kara da cewa duk wani mutum da ke da irin wannan makaman zai iya haddasa fitina a unguwa dungurumgum.

Ga dai bidiyon bindigun da aka gano a cikin babur din a kasa;

DUBA WANNAN: Arewa na halaka kanta da kanta - Sarki Sanusi II

A baya, kun ji cewa tsoron harin 'yan ta'adan kungiyar Boko Haram ya saka mata da yara da dama sun tsere daga kauyukan su sun yada zango a titunan Maiduguri.

Mutane a ƙalla 300 ne suka baro gidajensu a kauyen Kayamla da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno, sun ce sun baro gidajensu ne zuwa Maiduguri bayan an kai musu hari kuma suna ganin 'yan ta'addan za su sake kai musu harin.

Da su ke magana da wakilin The Punch a safiyar ranar Litinin, matan sun ce mazajensu ne suka turo su Maiduguri domin gujewa fada wa hannun 'yan ta'addan yayin da su kuma suka zauna a Kayamla.

Ɗaya daga cikin matan da ke kwana a titin kusa da sansanin horas da masu yi wa kasa hidima NYSC da aka mayar sansanin yan gudun hijira ta ce, "Mun shafe kimanin sati biyu muna nan, ba mu da zabi sai dai mu riƙa kwana a titi tunda an kore mu daga sansanin 'yan gudun hijiran."

Ta ce sun baro Maiduguri ne yayin da suka lura cewa akwai yiwuwar yan ta'addan za su sake kai musu hari.

Sai da daga bisani jami'an hukumar bayar da tallafin gaggawa na jihar Borno, BOSEMA, ta kwashe mutanen ta basu masauki a filin wasanni. Shugaban ta BOSEMA, Hajiya Yabawa Kolo ta ce za zarar gwamnati ta gama tantance halin da suke ciki za ta samar musu masauki a sansanin yan gudun hijirar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel