An kama dan banga tirmi da tabarya da matan abokin aikinsa a Ogun (Bidiyo)

An kama dan banga tirmi da tabarya da matan abokin aikinsa a Ogun (Bidiyo)

Wani dan banga a jihar Ogun ya dibo ruwan dafa kansa bayan da aka kama shi dumu-dumu yana lalata da matar abokin aikinsa.

Abokan aikinsa sun kama shi, sun saka masa ankwa sannan suka lakada masa dukkan tsiya bayan kama shi.

An yi awon gaba da shi bayan wasu mutanen unguwa sun roki ayi masa afuwa.

Ga bidiyon yadda lamarin ya kasance a kasa:

DUBA WANNAN: Wutan lantarki ta kashe shugaban masu tsaron Rotimi Amaechi a Kaduna

A baya, mun kawo muku cewa jami’an hukumar Hisbah na jihar Kano sun damke wani matashi da ake zargi da sayar da maganain gargajiya na kara karfin maza. Hukumar ta zargi mutumin da amfani da kalaman batsa wajen tallata hajarsa.

Mataimakin shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano din mai kula da ayyuka na musamman, Malam Muhammad Albakari, ya shaida wa BBC cewa matashin na amfani da kalmomin batsa ne yayin tallata hajarsa. Munin kalaman ya kai ga sai an runtse ido idan har mutum zai saurara.

Matashin na tallar maganin ne a kasuwar Kofar Wambai da ke tsakiyar birnin Kano din. Yana kuma amfani da amsa-kuwwa wajen jawo hankulan jama’a zuwa ga maganinsa.

Hukumar ta Hisbah ta bayyana cewa, yanayin kalamansa da yake amfani dasu wajen tallata magungunansa ba su dace ba amma daga bisani an sake shi bayan masa gargadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel