Wutan lantarki ta kashe shugaban masu tsaron Rotimi Amaechi a Kaduna

Wutan lantarki ta kashe shugaban masu tsaron Rotimi Amaechi a Kaduna

Mista Tony Iwelu, shugaban masu tsaron Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya rasu.

Mista Tony Iwelu, shugaban masu tsaron ministan sufuri, Mista Chibuike Rotimi Amaechi ya rasu ne sakamakon wutan lantarki da ta ja shi a bandakin otel dinsa da ke Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar 17 ga watan Fabrairun 2020 misalin karfe 10.30 na safe.

Iwelu ya tafi Kaduna ne tare da ministan domin tana Gwamna Nasiru El-Rufai murnar zagayowar ranar haihuwarsa yayin da hatsarin ya faru.

Wutan lantarki ta kashe shugaban masu tsaron Rotimi Amaechi a Kaduna
Wutan lantarki ta kashe shugaban masu tsaron Rotimi Amaechi a Kaduna
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan Hisbah sun damke mai maganin kara karfin mazakuta a Kano

Wani hadimin ministan ya tabbatar da rasuwar Iwelu amma ya nemi a sakaya sunansa domin ba a fitar da sanarwar rasuwar a hukumance ba kamar yadda Linda Ikeji Blog ta ruwaito.

Ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi ya karyata rade-radin cewa ya tsallake rijiya da baya a yayin da wasu 'yan bindiga suka kai farmaki a kan hanyar tashar jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja.

A cewar Amaechi babu yan bindiga ko masu garkuwa da mutane da suka kai masa hari.

Amaechi ya mayar wa jagorar fafutukar neman dawo da yan matan Chibok Aisha Yesufu martani, inda yace zagi ko cin mutunci ba zai sauya gaskiyar cewa babu wanda ya kai masa hari a Kaduna a daren jiya Lahadi.

Ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: “Baiwar Allah ba a kai min hari ba, ban ga wasu mahara, yan bindiga ko masu garkuwa da mutane ba kuma ban tsallake rijiya da baya ba, ban tsere ba..” zagi ko cin mutunci ba zai sauya gaskiyar cewa ba a kai min hari ba, a Kaduna a daren jiya.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel