Yanzu-yanzu: An kashe mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa a Abuja

Yanzu-yanzu: An kashe mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa a Abuja

Wasu makasa sun hallaka mataimakiyar diraktar gudanarwan fadar shugaban kasa, Laetitia Dagan, a gidanta dake Abua, fadar shugaban kasa ta bayyana.

Mataimakin dirkatan labaran fadar shugaban kasa, Attah Esa, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya sake inda ya ce an kashe Dagan ne misalin karfe 11 na daren Litinin.

Attah Esa ya bayyana cewa babbar ma'aikaciyar fadar shugaban kasan ta yi aiki a ofishinta zuwa misalin karfe takwas na dare amma zuwa 11 aka samu labarin kisan gillan da akayi mata.

Sakataren din-din-din fadar shugaban kasa, Jalal Arabi, wanda ya kai gaisuwar ta'aziyya ga iyalan maragayiyar ya siffanta a matsayin ma'aikaciya mai jajircewa na gaske.

Yanzu-yanzu: An kashe mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa a Abuja
Yanzu-yanzu: An kashe mataimakiyar diraktar fadar shugaban kasa a Abuja
Asali: Facebook

A bangare guda, Mun samu labari cewa an samu sabani tsakanin wasu Jiga-jigai a gwamnatin Buhari, inda NSA Babagana Monguno ya ke zargin Abba Kyari da yin ba-ba-kere a fadar shugaban kasa.

Janar Babagana Monguno mai ritaya ya na zargin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, da shiga tsakanin wasu Jami’an gwamnati da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Premium Times ce ta fitar da wannan rahoto na musamman a Ranar Litinin, 17 ga Watan Fubrairun 2020. Abin har ta kai Babagana Monguno ya nemi a daina sauraron Abba Kyari.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaron, ya rubutawa Shugabannin Hafsun Soji takarda su daina daukar umarni daga ofishin Abba Kyari wanda ake ganin ya na wuce gona da iri.

NSA Monguno ya na zargin cewa Abba Kyari ya na aikawa Hafsun Sojoji umarni ba tare da yarda ko sanin shugaban kasa ba, ana sa tunanin, wannan ya taimaka wajen tabarbarewar tsaro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel