Yaki da rashawa: Dan jaridar dake da hannu cikin satar N2.5bn ya yanke jiki ya mutu

Yaki da rashawa: Dan jaridar dake da hannu cikin satar N2.5bn ya yanke jiki ya mutu

Fitaccen dan jaridar nan, kuma shugaban kamfanin Pinnacle Communications Limited, Lucky Omoluwa ya yanke jiki ya fadi, ya sheka barzahu biyo bayan tuhumarsa da ake yi da hannu cikin badakalar satar kimanin naira biliyan 2.5.

Premium Times ta ruwaito iyalan Mista Omoluwa da wasu abokan aikinsu sun bayyana cewa Omuluwa ya mutu ne a babban asibitin kasa dake babban birnin tarayya Abuja, a ranar Talata, 18 ga watan Feburairu.

KU KARANTA: Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci bikin yaye sabbin jami’an EFCC a Kaduna

Yaki da rashawa: Dan jaridar dake da hannu cikin satar N2.5bn ya yanke jiki ya mutu
Omoluwa
Asali: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Omoluwa ya yanke jiki ya fadi ne gabanin fara shari’arsa da hukumar yaki da rashawa ICPC wanda take tuhumarsa tare da korarren shugaban hukumar watsa labaru ta kasa, Ishaq Kawu Modibbo da kulla wata badakalar cinikkayya inda suka sama da fadi da N2.5bn.

ICPC ta zargi Modibbo da Omoluwa da amfani da kamfanin Pinnacle, wanda ta shahara wajen sarrafa na’urorin watsa labaru, wajen shirya wannan badakala, hakan tasa a makon da ta gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Modibbo daga aikinsa.

Sai dai majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa Omoluwa ya yanke jiki ya fadi ne da sanyin safiyar Talata, daga bisani aka garzaya da shi zuwa babban asibitin kasa, inda a can ya rigamu gidan gaskiya.

Amma har zuwa lokacin tattara wannan rahoto asibitin bata fitar da wata sanarwa game da mutuwarsa ba, haka zalika kaakakin hukumar ICPC Rasheedat Okoduwa bata amsa kiraye kirayen da majiyarmu ta yi mata don jin ta bakinta game da batun rasuwar Omoluwa ba.

Shugaban kasa Muhaammadu Buhari ya kai ziyara jahar Kaduna domin halartar bikin yaye sabbin kananan jami’an hukumar EFCC, watau Detective Inspector Course karo na 5 a daya gudana a kwalejin horas da hafsoshin sojin Najeriya, NDA.

Bikin ya kawo karshen horo mai tsanani da jami’an suka samu a kwalejin NDA, wanda ake sa ran zai shirya sabbin jami’an don fuskantar kalubalen dake gabansu a harkar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

A cewar shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, EFCC ta hada kai da NDA ne domin horas da jami’an ta yadda ba zasu ji tsoron duk wani barazana da za’a musu a kan aikin yaki da rashawa ba, kuma ba zasu gajiya ba.

Da yake nasa jawabi a yayin biki, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sauye sauyen da suka gudanarwa a gwamnatinsa zasu kawar da duk wani kumbuya kumbuya da boye boye da ake yi a wajen harkar kudi a gwamnati.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel