Matashi dan asalin jihar Kano ya fito da fasahar koyon addinin Musulunci a waya

Matashi dan asalin jihar Kano ya fito da fasahar koyon addinin Musulunci a waya

- Wani matashin saurayi dan asalin Kano da yaje karatu kasar Uganda ya sanya mutanen Kano dana Najeriya baki daya alfahari da shi

- Matashin ya kirkiri wata fasaha ce da mutum zai iya amfani da ita wajen koyar addini a duk inda yake

- Matashin ya ce ya kirkiri fasahar ne domin ta dinga taimaka masa yana karatu a lokacin da yake hira da abokanan sa

A wani labari da muka samu a shafin yanar gizo na Sarewa Radio ya bayyana yadda wani matashin saurayi mai suna Ibrahim Mato Dangada, wanda yake dan asalin garin Dangada ne dake cikin karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano, ya kirkiri fasahar abin koyon karatun addinin Musulunci.

"Lokacin da na tafi kasar Uganda karatu, ina da wasu muhimman abubuwa da nake tattaunawa da abokanai na, kuma lokacin jarrabawa ta zo mini, sai nayi tunanin hada wani abu da zai kawo mini saukin karatu koda ina hira da abokanai na.

Matashi dan asalin jihar Kano ya fito da fasahar koyon addinin Musulunci a waya
Matashi dan asalin jihar Kano ya fito da fasahar koyon addinin Musulunci a waya
Asali: Facebook

"Ai kuwa sai na samu nasarar hada wani na saka masa littattafai nake karantawa, na kuma gwada naga yana yi sosai, bayan kammala jarrabawa sai na yi tunanin zan fito dana karatun addini, shine na zo da fasahar da mutum zai iya koyon karatun Hadisai, Fiqhu, Tsarki, da dai sauransu.

KU KARANTA: Hotuna: Dalibin makarantar sakandare a Najeriya ya kirkiri injin janareto da yake aiki babu fetir

"Za a iya amfani dashi wajen yin karatu kamar dai mutum yana hira da abokinshi, zai bashi umarnin irin littafin da yake so, shi zai nuno maka wadanda yake da su sai mutum ya zaba.

"Idan na samu na kara yawan littattafai zan wallafashi a shafukan sada zumunta kamar irinsu Facebook, Twitter da sauransu, sannan kuma ina so na samu mutane masu ilimin addini, musamman matasa da za mu yi aiki tare da su domin bunkasa abin ta fannoni da dama saboda ina da shiri sosai akn shi.

A lokuta da dama dai akan samu mutane masu fasaha da basirar kirkirar abubuwa wadanda ba mu da irinsu a Najeriya.

Amma matsalar rashin samun goyon baya na gwamnati ko kamfanoni ko kuma wasu masu hannu da shuni da irin wadannan mutane suke samu, sh yake sanyawa wannan basira ta su ta tashi a tutar babu.

A kwanakin baya mun kawo muku labarin wani matashi dan jihar Kano da ya kirkiri keke wanda ake yi masa caji.

Matashin ya kirkiri keken ne da yake tuka kanshi kamar babur, sannan kuma mutum zai iya amfani da jikin keken ya caja wayarshi ko kuma na'ura mai kwakwalwa, wato 'Laptop' a turance.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel