Za mu maka Buhari gaban kotu a kan wa’adin manyan hafsoshin tsaro – Falana
Babban lauya mai zaman kansa, Femi Falana ya bayyana cewa za su shigar da kara gaban kotu domin tilasta ma shugaban kasa Muhammadu Buhari tsige manyan hafsoshin tsaron Najeriya bisa dalilin karewar wa’adinsu.
Falana ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Channels, inda yace haramun ne shugaban kasa Buhari ya kara ma hafsoshin tsaron wa’adin mulki, don haka yace sun ci lokacinsu.
Sai dai da aka tambaye shi me yasa ba’a kalubalanci gwamnatinba idan da gaske yake sai yace: “Ina tabbatar maka cewa a yanzu haka akwai shirin da ake yin a shigar da gwamnati kara game da wannan batu.”
KU KARANTA: Jiragen yakin Najeriya sun yi watsa watsa da sansanin yan Boko Haram a Borno
Falana ya kara da cewa a zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, karamin ministan kwadago na gwamnatin Buhari, Festus Keyamo ya taba kai gwamnati kara a kan cewa lallai majalisa ce ya kamata ta tabbatar da manyan hafsoshin tsaro kafin shugaban kasa ya nada su.
Kuma kotu ta yanke hukuncin cewa lallai yana da gaskiya, har ma Alkalon kotun yayin da yake yanke hukunci ya bayyana cewa lallai sai majalisa ta amince da nadin hafsoshin tsaro kafin a rantsar dasu, don haka Falana yace idan har majalisa ke da ikon amincewa dasu kafin a nadasu, lallai dole ne sai an nemi amincewartra kafin a kara musu wa’adin mulki.
“Hakan yasa a lokacin da majalisar wakilai ta umarci hafsoshin tsaro su yi murabus, kamata ya yi ta dogara da wannan hukuncin, sai ta fada ma shugaban kasa cewa tunda dai ba zaka iya nadawa ba tare da amincewarmu ba, toh ba haka zalika ba zaka iya kara musu wa’adi ba tare da amincewarmu ba.” Inji shi.
Daga karshe Falana ya tabbatar da cewa shugaba Buhari ya karya doka, saboda a cewarsa ta yaya za’ayi ma ma’aikata ritaya daga aiki da zarar sun yi aikin shekaru 35, amma kuma a cigaba da kara ma wasu wa’adin mulki?
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng