Tashin hankali: Kasar Koriya ta Arewa ta fara kashe mutanen dake dauke da Coronavirus

Tashin hankali: Kasar Koriya ta Arewa ta fara kashe mutanen dake dauke da Coronavirus

- Kasar Korea ta arewa ta kashe wani mai cutar coronavirus sakamakon fita da yayi cikin jama’a bayan an killace shi

- Jami’an tsaro ne suka damke mara lafiyan kuma aka harbe shi a matsayin hanyar daukar matakin hana yaduwar muguwar cutar

- Gwamnatin kasar Korea ta arewa ta dau tsauraran matakai a kan yakar cutar ta yadda take killace duk wanda ya dawo daga kasar China

Kasar Korea ta arewa ta kashe wani mai cutar Coronavirus sakamakon fita da yayi bayan an killace shi. Shugaban kasa Kim Jong-un baya wasa da cutar don ya dau manyan matakai a kan ta.

Jami’an tsaro ne suka damke mara lafiyan kuma aka harbe shi a matsayin hanyar daukar matakin hana yaduwar muguwar cutar.

Jaridar Dong-a ta kasar Korea ta arewa ta bayyana yadda aka ware wani jami’in gwamnati bayan ya dawo daga kasar China. Shugaban kasar ya saka dokokin rundunar soji ne don tabbatar da an hana yaduwar cutar duk da kuwa har yanzu ba a samu ko mutum daya da ita ba.

Tashin hankali: Kasar Koriya ta Arewa ta fara kashe mutanen dake dauke da Coronavirus
Tashin hankali: Kasar Koriya ta Arewa ta fara kashe mutanen dake dauke da Coronavirus
Asali: UGC

Kasar China ta shiga muguwar damuwa bayan da muguwar cutar ta kashe mutane 242 a cikin sa’o’I 24. Jami’an lafiyar kasar sun ce hakan ya faru ne bayan da suka sauya yadda suke duba cutar.

KU KARANTA: Tirkashi: Uwa da 'Ya sun haihu a lokaci daya bayan wani ya dirka musu cikin shege

Kusan dai mutane 15,000 ne suka kamu da cutar a yankin Hubei zuwa ranar Alhamis da ta gabata. Shugaban cibiyar kiwon lafiya ta Hubei din ya ce mutane 242 ne suka rasa rayukansu a ranar Laraba wanda hakan ya bayyana mafi yawan mutuwa sakamakon cutar a rana daya.

Jami’an kiwon lafiyar kasar Korea ta arewan na ware mutum ne matukar aka gano ya je kasar China. Wani jami’in gwamnati kuwa an rufe shi a gidan gonar shi ne bayan da aka gano ya je kasar China din amma yana boyewa.

A jiya ne Pyongyang ya sanar da cewa an mayar da tsawon kwanakin killace mutane zuwa kwana 30, rubi biyu a kan yadda cibiyar lafiya ta duniya ta bukata. Ana kuma bukatar cibiyoyin gwamnati da bakin haure da su kiyaye dokokin kasar Korea ta arewa, kamar yadda kafafen yada labarai suka sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng