Tirkashi: Uwa da 'Ya sun haihu a lokaci daya bayan wani ya dirka musu cikin shege

Tirkashi: Uwa da 'Ya sun haihu a lokaci daya bayan wani ya dirka musu cikin shege

- Wata mata mai shekaru 38 ta fada bakin ciki bayan da suka haihu a jere da ‘yarta kuma daga namiji daya

- Mildred ta fada bakin ciki ne bayan da ta gano diyarta na dauke da ciki, amma sai ta fada firgici bayan ta gano namiji daya ne yayi musu ciki

- Uwa da ‘yar sun haifa yara maza ne amma tsakaninsu kwanaki hudu kacal

Wata mata ‘yar asalin kasar Afirka ta Kudu mai suna Mildred Mashego da diyarta mai suna Patricia sun shiga tarihin duniya na yadda suka haifawa namiji daya ‘ya’ya a cikin mako daya.

Jaridar Times Live ta ruwaito yadda matar mai shekaru 38 da ke Casteel a kasar Afirka ta kudu ta samu ciki bayan diyarta mai shekaru 19 ta samu ciki.

Fushin da ta shiga ya koma firgici bayan ta gano cewa mutum daya ne ke da cikin da ke jikinta da na jikin ‘yarta.

Tirkashi: Uwa da 'Ya sun haihu a lokaci daya bayan wani ya dirka musu cikin shege
Tirkashi: Uwa da 'Ya sun haihu a lokaci daya bayan wani ya dirka musu cikin shege
Asali: Facebook

Patricia ce ta fara haifar yaro namiji sannan mahaifiyarta ta haifa nata bayan kwanaki hudu. Namijin mai kwazo mai suna Vincent Malumane ya amince shi ke da yaran bayan ya bayyana cewa a sirrance ya kwanta da uwar sannan ya bi diyar. “Ba zan iya komawa ba yanzu don bayanin abinda ya faru.” Ya ce.

KU KARANTA: Allah Sarki: Saurayi ya kashe kanshi, bayan budurwar da ya dauki nauyin karatun ta gaba daya ta fara shirin auren wani saurayi daban

“Abinda zamuyi yanzu shine mayar da hankali wajen ganin yaran sun tashi cikin koshin lafiya da tarbiya.” In ji mahaifiyar.

Mildred wacce ita ce mahaifiyar ta fada tsananin bakin ciki bayan da ta gano cewa ‘yarta na da ciki. Amma ta shiga babbar damuwa bayan da ta gano cewa namiji daya ke da cikin don kuwa har ta fara zancen zubarwa.

Amma kuma bayan an haifa jariran, Mildred ta yanke hukuncin yafewa ‘yarta albarkacin jikanta. A halin yanzu dai sun mayar da hankali wajen rainon ‘ya’yan amma kuma suna tunanin abinda zasu sanar dasu bayan sun girma a kan mahaifinsu.

Dukkan matan sun ce basu mu’amala da Vincent amma ya jaddada cewa yana tare da mahaifiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng