Bokan da yake bawa maza maganin mata ya sume bayan ya iske budurwarshi da wani kato suna iskanci

Bokan da yake bawa maza maganin mata ya sume bayan ya iske budurwarshi da wani kato suna iskanci

- Wani kwararren mai maganin gargajiya da yake ba wadanda aka ci amanarsu maganin waraka daga kunar zuciya ya fada tarkon mace

- Mai maganin ya fadi magashiyyan ne a safiyar Laraba inda ya fada doguwar suma sakamakon kama budurwar shi da yayi da wani saurayi

- Paa Dogo a halin yanzu yana babban asibitin Effia Nkwanta da ke Ghana bayan ihun da ya zabga na ganin wani kato kwance da masoyiyar shi

An kwantar da wani kwararren mai maganin gargajiya a asibiti a safiyar Laraba bayan budurwar shi ta ci amanar shi. Ba wannan bane abin mamakin, mai maganin ya kware da bada maganin ciwukan da suka shafi zuciya da kuma hauka a yankin Sekondi da ke Yammaci.

A halin yanzu dai mai maganin gargajiyar na kwance a asibitin Effia Nkwanta da ke yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa ana sauran kwanaki biyu bikin ranar masoya wanda ake yi a ranar 14 ga watan Fabrairu, sanannen Paa Dogo ya je gidan budurwar shi don kai mata fure amma sai ya tarar da ita kwance a gado da saurayinta.

Jaridar Adomonline ta ruwaito cewa wasu mazauna yankin sun gano cewa mai maganin gargajiyar ya fada soyayyar wata ma’aikaciyar jinya ce wacce ba a dade da turota garin ba.

Ya fara haduwa da ita ne bayan da aka tura ta wajen Paa Dogo karbar maganin cutar da ta addabeta.

KU KARANTA: Majalisar dattijan kasar Utah za ta halsta auren mace fiye da daya

Wata mazauniyar yankin mai suna Maame Pokua ta ce da farko dai ma’aikaciyar jinyar ta gano cewa saurayinta na soyayya da kawarta wanda tayi kokarin kashe kanta a kan hakan. Daga nan ne aka tura ta wajen Paa Dogo don samun magani. Paa Dogo kuwa ya kware wajen bada maganin irin wadannan cutukan har da na hauka.

Bayan da Paa Dogo ya ba ta maganin abinda yake damunta, sai ya fara sonta tare da siya mata abubuwa masu tsada. Ya mika kokon barar soyayya kuma ta karba.

“Bayan makonni kadan da fara soyayyar ne ya je kai mata furanni inda ya tarar da ita tare da tsohon saurayinta suna shagali. Paa Dogo ya fasa ihu tare da cewa ‘Yesu, na mutu.” Maame ta ce.

Daga nan ne aka kwashe shi sai asibitin Effia Nkwanta da ke yankin bayan ya fada doguwar suma. A halin yanzu yana karbar taimakon gaggawa daga likitoci kamar yadda jaridar Pulse. Ng ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel