Harin Katsina: Yan fashi sun kwace jarirai, sun jefa cikin wuta a gaban iyayensu

Harin Katsina: Yan fashi sun kwace jarirai, sun jefa cikin wuta a gaban iyayensu

Shugaban karamar hukumar Batsari dake Jihar Katsina a ranar litinin ya bayyana yanda harin da aka kai musu a makon da ya gabata ya haddasa kisan mutane da yawa a yankin.

Akalla Mutane 30 suka rasa rayukansu a cikin kauyen Tsawwa da Dankar.

An bayyana cewa daga cikin mutane 21 da aka kashe a garin Tsauwa, bankawa 13 wuta akayi har lahira.

“Yan fashin sun kwace jarirai sun jefa wuta a gaban iyayen su,” Shugaban Kauyen,Ibrahim Zangina ya bayyana wa Gwamna Aminu Bello Masari yayinda ya kai ta’aziya ga wanda suka tsira.

Bisa ga bayaninshi, Yan fashin sun shiga kauyen haye kan Babura kimanin 180 duk dauke da akalla mutum biyu zuwa uku sannan suka fara harbin duk wanda suka ci karo da shi.

Ya kara da cewa harin ya faru ne yayinda ake sallar la’asar inda yace “Sun harbi mafi akasarin masu alwala.“

“Sun harbi dabbobi da dama sannan sun kona amfanin gona, bamu taba fuskantar harin yan fashi irin wannan ba. A cewar sa.

KU KARANTA Ganduje ya nada hadimai 3 na musamman akan aikin fitilun haska titi

Har wa yau, Shugaban Kauyen Dankar, Muhammad Suhura, ya bayyanama Masari cewa wasu daga cikin jama’an kauyen sun tsira akan dabbobin su.

Masari yayi Allah wadai da lamarin sannan ya roki wadanda suka bar kauyen dasu dawo.

Gwamnan ya bayyana cewa basuyi garkuwa da kowa ba amma anyi asarar rayuka da amfanin gona.

Yace gwamnati zata dauki mataki kuma kuma ya tabbatar da cewa hakan bazai sake faruwa ba, kuma ya dauke shi a matsayin kaddara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel