Ganduje ya nada hadimai 3 na musamman akan aikin fitilun haska titi

Ganduje ya nada hadimai 3 na musamman akan aikin fitilun haska titi

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya nada hadimai na musamman uku akan abinda ya shafi fitilun tituna a fadin jihar.

A wata wasika a ranar 13 ga watan Febrairu, sakateran jihar ya sanar da Anwalu Salihu akan nadinsa na Shugaba na musamman akan aikin fitilar titi”

Bisa ga wasikar, an nadasa ne kan jajircewarsa akan aiki, da kuma rikon gaskiya.

“Wannan ya iso gareka ne daga Mai girma gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda ya tabbatar da nadinka akan zama hadimi na musamman kan fitilun titi kuma aikin zai fara gudana a ranar 10 ga watan Febrairu, 2020” cewar wasikar.

“Wannan nadin gaskiya da amanar, an gina shi ne akan lura da jajircewa akan aiki,kwarewa,da biyayyarka. Kuma muna fata zaka yi amfani da wadannan dabi’u wurin aiwatar da aikin.“

A wata hirar wayar tarho ranar Litinin, Salihu Yakasai, ya tabbatar da cewa an nada mutane uku na musamman akan fitilar titi.

Ya bayyanawa manema labarai cewa wadanda aka nadan zasu hallaru ne wurin kwamishanan aiki ba kai tsaye wurin gwamna ba.

Yakasai ya bayyana cewa zasu rika lura da abubuwan da suka ya shafi janareto da man gas wa’inda ake amfani dasu wurin fitilun.

Ganduje ya nada hadimai 3 na musamman akan aikin fitilun haska titi
Ganduje ya nada hadimai 3 na musamman akan aikin fitilun haska titi
Asali: Facebook

A bangare guda, Yayinda Manyan kasa suka kai ziyara wurin gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El_Rufa’i a ranar murnar zagayowar haihuwar shi, lauyansa, AbdulHakeem Mustapha SAN yace El-Rufa’i nada satifikate 83 na Jami’ar Havard a Amurka.

Mustapha SAN yace yayi mamaki ranar da yaga satifikate din El-Rufa’I.

Yace, “Akwai wani lokaci da aka kai El-Rufa’I kotu saboda rashin satifikate. A hanyar zuwan mu kotun ranar, ya dauke ni a motarshi sannan ya mika mun wata ambulaf.“

“Yayinda na bude ambulaf din, sai na ga yana da satifikate guda 83 na Jami’ar Havard. Sai nace mai daga ina wadannan? Sai yace Lokacin da sa’annina suke siyan manyan motoci, gidaje da ababen sha’awa, ni kuma ga abinda nayi da kudina.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel