Bikin cika shekaru 60: El-Rufa’I nada satifikate 83 daga Jami’ar Harvard - Babban Lauya

Bikin cika shekaru 60: El-Rufa’I nada satifikate 83 daga Jami’ar Harvard - Babban Lauya

Yayinda Manyan kasa suka kai ziyara wurin gwamnan Jihar Kaduna,Malam Nasir El_Rufa’i a ranar murnar zagayowar haihuwar shi, lauyansa, AbdulHakeem Mustapha SAN yace El-Rufa’i nada satifikate 83 na Jami’ar Havard a Amurka.

Mustapha SAN yace yayi mamaki ranar da yaga satifikate din El-Rufa’I.

Yace, “Akwai wani lokaci da aka kai El-Rufa’I kotu saboda rashin satifikate. A hanyar zuwan mu kotun ranar, ya dauke ni a motarshi sannan ya mika mun wata ambulaf.“

“Yayinda na bude ambulaf din, sai na ga yana da satifikate guda 83 na Jami’ar Havard. Sai nace mai daga ina wadannan? Sai yace Lokacin da sa’annina suke siyan manyan motoci, gidaje da ababen sha’awa, ni kuma ga abinda nayi da kudina.”

Bikin cika shekaru 60: El-Rufa’I nada satifikate 83 daga Jami’ar Harvard - Babban Lauya
Bikin cika shekaru 60: El-Rufa’I nada satifikate 83 daga Jami’ar Harvard - Babban Lauya
Asali: Facebook

KU KARANTA Dalilin da yasa Buhari ba zai canza hafsoshin tsaro ba - Fadar shugaban kasa

Daga cikin wadanda suka halarci taron sune Shugaban majalissar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, da Ministan Sufuri,Rotimi Amaechi,.

Hakazalika akwai Ministar Kudi Zainab Shamsuna Ahmad, Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomole, Tsohon shugaban APC, Cif Odigie Oyegun da kuma tsohon Shugaban Gwamnan Jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ne suka halarta.

Sauran sune : Sarkin Ife,Oba Adeyeye Ogunwusi, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da Shugabar hukumar tashar jirgin ruwa, Hadiza Bala Usman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel